Ticker

6/recent/ticker-posts

Bishiyar Zumunci

1. Rabbana ka ji ƙan zumunci,

  Don a yau mun ruguza shi.

 

2. Babu mai duba gare shi,

  Ko ya ce zai ɗabbaka shi.

 

3. Ga shi Allah yai bayani,

  Kansa domin mu riƙe shi.

 

4. Ya yi alƙawari na narko,

   Gun waɗanda suke katse shi.

 

5. Ɗaha ya yi kira gare mu,

   A Hadisai don mu yo shi.

 

6. Ya faɗo falalar zumunci,

  Da azaba in ka ƙi shi.

 

7. Yau idan ka tsaya ka duba,

   Duka ba ma aikata shi.

 

8. Mun yi watsi da zumunci,

 Babu mai neman a yo shi.

 

9. Har iyaye namu mata,

   Da yawa sun bar batun shi.

 

10. Ba su yinsa saboda Allah,

Ya zamo tamƙar farashi.

 

11. Wanda yai shi za su yi wa,

  Sun cire Allah cikin shi.

 

12. Wasu dangi ne guda ɗai,

 Babu wanda ya yo zaton shi.

 

13. Ɗan'uwa ne shi na wane,

 Ko idan an tambaye shi.

 

14. Kuma wando nasu ɗai ne,

   Gun zumunci ba su yin shi.

 

15. Wani wa ne da ƙaninsa,

  Kan kudi suka tarwatsa shi.

 

16. Rabbana ka ji ƙan mutan da,

Gun zumunci babu ƙyashi.

 

17. Su a loton ba salalu,

  Ga zumunci sun riƙe shi.

 

18. Za su ɗau harama a jaki,

Duk gari sun zagaya shi.

 

19. A yi ziyara a yi zumunci,

   Ba su cewa wane ba shi.

 

20. Suka rayuwa cikin sallama,

Arziki aka yalwata shi.

 

21. Mu ko yanzu idan ka duba,

  Ba zumunci mun kashe shi.

 

22. Shi ya sa yau ba lumana,

Ga talauci ya yi goshi.

 

23. Ga masifu sun yawaita,

   Tun da mun ƙi faɗin na Arshi.

 

24. 'Yan uwana sai mu tuba,

   Mu yi zumunci ban da ƙyashi.

 

25. Kar mu ware guda a dangi,

   Ko mu ce ai wane ba shi.

 

26. Muyi zumunci don Azizu,

Don mu tsira a ranar tashi.

 

27. Nan nazo ƙarshen kasidar,

Wacce nayi akan mu tashi.

 

28. Watakil wani zai su'ali,

  Wa ya yo baiti da shi - shi.

 

29. Ɗanbala suna Mohammed,

   Can a Borno cikin garin shi.

 

30. A watan Ramadana yai yo,

   Sha biyu ga wata batun shi.

 

31. Hijirar sha huɗu arba,

 Da huɗu a cikin yabon shi.

 

32. Wanda yai daidai da ukku,

  Ga watan April ku ji shi.

 

33. Ashirin, Ashirin da ukku,

   Haihuwar Isa ogan shi.

 

34. Rabbana ninku salati,

Gun mafi daraja da kamshi.

 

35. Alihi nasa har Sahabu,

Sun bi Annabi babu kaushi.


 www.amsoshi.com

Na:

Mohammed Bala Garba
12 Ramadan, 1444.
3 April, 2023.

Post a Comment

0 Comments