Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Kinaya/Siffantawa
Salon
kinaya shi ne salon da Ɗangambo ya kira
siffantawa, wato salon da ake amfani da shi a kira wani da sunan wani da ba shi
ba da nufi mai saurare ko karatu ya dubi wannan abin da kwarjini ko saɓanin haka na wancan abin da aka
kira shi da sunansa, Yahya (1997). Kinaya kwatance ne na kaitsaye ta hanyar
cire kalmomin kwatance da akan shigar tsakanin abin da aka kwatanta da wanda
aka kwatanta shi da shi, irin su kamar, sai ka ce, ya fi, da sauransu. Akwai
iri wannan salo a cikin waƙoƙin bara. Misali:
Da bara da bara
dan malam,
Almajiri
tsuntsu ne,
Da ya ji motsin
tsaba,
Sai ya yi hiringi
da kunne,
(Da bara da bara Ɗan Malam)
A cikin wannan layi na biyu an
siffanta almajiri da tsuntsu ta wajen son tsaba. Wato yadda tsuntsu ke son
tsaba yake mayar da hankalinsa wajen da ya ji take, haka nan almajiri yake ba
su da bambanci ko kaɗan. A
haka wannan ɗa na waƙa yake son a dubi almajiri, mutum mai son ƙoto koyaushe daidai da yadda tsuntsu ke da bukata da shi
koyaushe. Almajirai suna faɗin haka
domin masu sauraren waƙarsu (waɗanda ake yi wa bara) su san irin
tsananin bukatar abinci da masu baran suke da ita. Ƙila haka ya sa a tausaya a ba su sadaka. A wani misalin kuma cewa ake yi:
Ina masoyan Muhammadu,
In na ci na sha Muhammadu,
Ina kirarin Muhammadu,
Madara da zuma Muhammadu,
(Madara da zuma Muhammadu)
A
wannan waƙar ma layi na ƙarshe
salon kinaya ne, inda aka kira Annabi Muhammadu da madara da zuma. A nan mai waƙar na son mai saurarensa ya riya a ransa yadda madara
take da daɗi idan
aka saka zuma a cikinta. To irin daɗin wannan daɗin haɗin da ya sani haka Annabi yake da
daɗi ga Musulmi.
Duk da yake daɗin
Annabi ya fi ƙarfin haka, ya
kawo wannan ne a matsayin abin shan da yake gani ya fi soyuwa ga mutum.
Haka a
wannan ɗan waƙa mai zuwa shi ma akwai kinaya a cikinsa. Ga abin da ake
cewa:
Jirgi Ɗan
Amina alƙawalin duniya,
Allah ya yi duniya ya yo lahira,
Ita waccan ta lahira can muka dogara.
(Jirgi Ɗan Amina)
A
farkon ɗan wannan waƙa ne salon kinaya ya fito, wato wajen da aka kira Annabi
da sunan jirgi. Abin nufi a nan shi ne, yadda jirgi ke kwasar ayarin jama’a ya
tsallakar da su daga haɗarin
ruwan kogi, haka Annabi ke kuɓutar da al’umma daga ɓata da
haɗarin shiga
wuta. Mawaƙin na son mai saurarensa ya dubi Annabi irin dubin jirgin
da ya loda al’umma ya ratsa kogi da su ya kai su ganga lami lafiya ba tare da
samun wani haɗari ba.
Idan aka lura da dukan misalan da suka gabata, za a ga kwatanta Annabi ne ake
da waɗannan abubuwa,
amma saboda tsananta kwatancen sai aka share kalmomin kwatancen aka yi
kinayarsu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.