Ticker

6/recent/ticker-posts

Kanoma

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Kanoma

 

  G/Waƙa: Kanoma  ka fi ƙarhin gida,

: Abu mai turu.

 

  Jagora: Eh ƙwarai

  ‘Y/ Amshi: Kanoma  ka fi ƙarhin gida,

: Abu mai turu.

 

  Jagora: Kai na ji daɗi ƙwarai.

 ‘Y/ Amshi: Kanoma ka fi ƙarhin gida,

: Abu mai turu.

 

 Jagora: Mazaje ku kama noma x2.

 ‘Y/ Amshi: Kowa  yak ki noma,

: Wuya na cim mai.

 Jagora: In taƙamak ka iko,

: Kai ko doki dubu garai,

: Ga bayi,

 ‘Y/ Amshi: Sai  an kai maka damu[1] ka sha.

 

 Jagora: In  taƙamak iko kai ko,

: Doki dubu garai ga bayi.

 ‘Y/ Amshi: Sai  an kai maka damu ka sha,

 

 Jagora: In taƙamak ka ilmi ba’a,

: Karatu a kammale baki dai.

‘Y/ Amshi: Sai an aje damman gero nai.

 

Jagora: Kowa ya aje gero ya,

: Aje dawa ya aje damman,

: Maiwa’ ita!

‘Y/ Amshi: Wannan ya wuce renin kowa .

 

Jagora: Shi wanda baya da gero,

: Baya da kuɗɗin sayen,

: Abinci ko ɗai.

‘Y/ Amshi: Sai dai ya karkace baki ɗai.

 

Jagora: Kara Bala da sauƙi.

‘Y/ Amshi: Ashe bana ya ji wuya,

: Ba daɗi.

 

Jagora: Wane tsiya ta sa mashi taggo[2].

‘Y/ Amshi: Ta yi baki irin kama da koren kaiwa.

 

Jagora: Ka bari sai da dagumi yaka arya,

: Karya .

‘Y/ Amshi: Sai  babu na dagumi ya ba  karya.

 

 Jagora: In kash shigo ga birni ka ishe kowa,

: Da na shi bindi x2.

 ‘Y/ Amshi: Samu ko zan gar niya,

: Ka so ka baya kaima ,

: Ka zama dud da sauran,

: Ka ji wuyar maza da aikon gona x2.

 

Jagora: Ko ban san ka,

: Ko da na goye ba bai x2.

‘Y/ Amshi: Kazo sarki ga katon banza x2.

 

Jagora: Allah shi waddan duhun yara.

‘Y/ Amshi: Sannun da aiki da yai ko bai zoba,

: Ka ji wuyar maza ka yi aikin gona ,

 

Jagora: Tashin tsiya  ba ni labarin,

: Ta ce da kasa da geme.

‘Y/ Amshi: Duka da yar sun ka,

: Banbanta mai,

: Kai maza sun ka,

: Maimaita ma x2.

 

 Jagora: Yau dai ga Aliyu ya  ba ni doki.

‘Y/ Amshi: Yanzu noma yaka kari,

: Dai dai.

 

Jagora: Kai na gaban  su da  duki,

: Sannu da aiki.

‘Y/ Amshi: Yan zu noma ya kari ko,

: Dai .

 

 Jagora: Duk kai duro kay yi mata. 

‘Y/ Amshi: Ya  barman abu da ƙwaryar nono.

 Jagora: Ga ta da raina wata mata.

‘Y/ Amshi: Ya  barman abu da ƙwaryar nono.



[1] Fura musamman furar gero.

[2]  Tufafi tagguwa kamar yadda Sakkwatawa suke cewa, ma’ana riga.

Post a Comment

0 Comments