Ticker

6/recent/ticker-posts

Ali Na Mani Kotoko

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ali Na Mani  Kotoko

G/Waƙa: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.

 

Jagora: Da nit taho an ce,

: Ya taji gona tun sahe,

  ‘Y/Amshi: Yana cikin daji,

: Ya tahi gona gun kaibe[1],

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.

 

Jagora: Mai son dawa kyauta,

: Ya biyo hanyar Wasagu.

‘Y/Amshi: Ya iske jan zaki,

: Ali na Mani  ɓangallai[2].

 

Jagora: Mai son dawa kyauta,

: Ya biyo hanyar Wasagu.

  ‘Y/Amshi: Ka iske jan zaki,

: Ali na Mani  ɓangallai,

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.

 

Jagora: Ina cikin Maru zanne,

: Sai ga mota shahe.

‘ ‘Y/Amshi: Ga buhu goma,

: Da ni da ɗiyana mui gari.

 

Jagora: Ina cikin Maru zanne,

: Sai ga mota shahe.

‘Y/Amshi: Ga buhu goma,

: Da ni da ɗiyana mui gari,

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.

 

Jagora: Sarkin noman ste,

: Na Sakkwato sosai.x2

  ‘Y/Amshi: Ali gwanki sha bara.x2

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.

 

Jagora: Ka ga mun koma,

: Mazanmu masu yaƙin huɗa.

  ‘Y/Amshi: Babu kamar zaki,

: Ali na Mani  ɓangallai.

 

 Jagora: Kaduna mun koma,

: Mazanmu masu yaƙin huɗa.

  ‘Y/Amshi: Babu kamar zaki,

: Ali na Mani  ɓangallai,

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.

 

Jagora: Maza ku kama noma ku riƙa,

: Ta kai ƙunƙa yanzu.

  ‘Y/Amshi: Kwano ya kai nera[3],

: Ga raggo na kwance,

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.x2

 

 Jagora: Da nit taho ance,

: Ya tahi gona tun swahe[4].

‘Y/Amshi: Yana cikin daji,

: Ya tahi gona gun kaibe.

 

 Jagora: Gandun Ali ya yi gandu sosai,

: Ga hwaɗi ga dwaya.

  ‘Y/Amshi: Ko’ina Ali ya koma,

: Ya kai mil[5] hamsin.

 

Jagora: Gandun Ali ya yi gandu sosai,

: Ga hwaɗi ga dwaya[6].

Y/Amshi: Ko ina Ali ya koma,

: Ya kai mil hamsin.

 

Jagora: Ɗaiwajje[7] ga shanu.

  ‘Y/Amshi: Ɗaiwajje  ga kaji.

 

 Jagora: Sashe matan aure.

  ‘Y/Amshi: Ɗaiwajje karuwai.

 

Jagora: Sashe matan aure.

  ‘Y/Amshi: Ɗaiwajje[8] karuwai.

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki Ali na Mani  Kotoko.

 

Jagora: Ga masallaci ya yi

: Ga ruwan alwalla.

  ‘Y/Amshi: Lokacin aiki,

: Don a hito aiki sosai.

 

Jagora: Ga masallaci ya yi,

: Ga ruwan alwalla.

  ‘Y/Amshi: Lokacin aiki,

: Don a hito aiki sosai.

 

 Jagora: Can nig ga guguwa ta murzo.

  ‘Y/Amshi: Ta ɗauko sansami,

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa.

 

Jagora: Can nig ga guguwa ta murɗo.x2

  ‘Y/Amshi: Ta ɗauko sansami[9].x2

 

Jagora: Gahwara yaro,

: Kar ya yi ma aikin wota.x2

  ‘Y/Amshi: Ya ɓangalo laka,

: Duk ta ruhe ma kahwaɗɗu.

: Ba da kai aka wargi ba,

: garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.x2

 

Jagora: Ɗanmalka mai jikin ƙarhe.

  ‘Y/Amshi: Ka ɗara shanu jan galma,

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa.

 

Jagora: Ɗan malka mai jikin ƙarhe.

  ‘Y/Amshi: Ka ɗara shanu jan galma,

 

 Jagora: Mai gero mai dawa.

  ‘Y/Amshi: Mai gujiya mai kaɗa.

 

 Jagora: Mai gero mai dawa.

  ‘Y/Amshi: Mai gujiya mai kaɗa[10].

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki Ali na Mani  Kotoko,

 

 Jagora: Maza ku kama noma ku riƙa,

: Ta kai ƙunƙa[11] yanzu.

‘Y/Amshi: Kwano ya kai nera,

: Ga raggo na kwance.

 

Jagora: Malan Adamu na gode mai,

: Yai ma aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani  ɓangallai.

 

Jagora: Malan Adamu na gode mai,

: Yai ma aikin ƙwazo,

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani  ɓangallai.

 

Jagora: Gilbaɗi na gode mai,

: Yai man aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani  ɓangallai.

 

Jagora: Ladan Gilbaɗi na gode mai,

: Yai man aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani  ɓangallai,

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.x2

 

  Jagora: Alhaji Adamu ina gode mai,

: Yai man aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani  ɓangallai.

 

Jagora: Alhaji Adamu ina gode mai,

: Yai man aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani ɓangallai[12].

 

Jagora: Ladan Abubakar na gode,

: Yai man aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani  ɓangallai.

 

 Jagora: Isah direba na gode mai,

: Yai man halin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yabban,

: Dan ka na Mani  ɓangallai.

Jagora: Isah direba na gode mai,

: Yai man halin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yabban,

: Don ka na Mani  ɓangallai.

 

Jagora: Hadda Mamman Sani,

: Yai man aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani  ɓangallai.

 

Jagora: Sani ɗan Hure na gode mai,

: Yai man aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yabban,

: Don ka na Mani  ɓangallai.

 

Jagora: Malan tumba na yaba mai, 

: Yai man aikin ƙwazo.

  ‘Y/Amshi: Abinda duk yab ban,

: Don ka na Mani  ɓangallai,

: Ba da kai aka wargi ba,

: Garin yaƙin huɗa,

: Maganin aiki,

: Ali na Mani  Kotoko.x2



[1]  Sharar gona.

[2]  Mai ɓangalar laka wajen noma.

[3]  Naira ɗaya. Wato kuɗin da ake sayar da tiyar dawa kenan a lokacin da aka yi waƙar.

[4]  Da safe.

[5]  Mile, wato kimanin faɗin wurin.

[6]  Kasar noma mai albarka

[7]  Wani ɓangare.

[8]  Wani ɓangare.

[9]  Hakukuwa da wasu tarkacen da iska kan kwaso.

[10]  Auduga

[11]  Maƙura, idan abu ya tuƙe.

[12]  Faskacen laka da babbar fartanya sukan mulmulo idan ana noma.

Post a Comment

0 Comments