Ticker

6/recent/ticker-posts

Audi Baturen Gonag Gusau

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Audi Baturen Gonag Gusau

 

  G/Waƙa: Ko can aiki shi yat tsara,

: Audi baturen gonag Gusau.

 

  Jagora: Ko can aiki shi yat tsara,

: Audi baturen gonag Gusau.

 ‘Y/ Amshi: Ko can aiki shi yat tsara,

: Audi baturen gonag Gusau.

 

  Jagora: Audi kai ne ba su ne ba na Garba .

  ‘Y/ Amshi: Darajjar malan ya taimaka.

 

  Jagora: Isah wamban Kware nag ode mai.

 ‘Y/ Amshi: Darajjar malan ya taimaka.

 

 Jagora: Kaka magaji ina gode mai

‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka.

 

 Jagora: Alhaji Garge ina gode mai,

‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka.

 

Jagora: Alhaji Garge yana kyauta man.

‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka.

 

Jagora: Yahaiya Ambursa na yaba mai ƙwazo,

‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka.

 

 Jagora: Godiya malan Bello.

‘Y/ Amshi: Ya yi man bajinta don mi ya taimaka.

 

 Jagora: Malan Isihu nag ode mai.

‘Y/ Amshi: Darajjam[1] malan ya taimaka.

 

Jagora: Tukur na waliyi nag ode mai,

  ‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka.

: Ko can aiki shi yat tsara,

: Audi batureb gonag Gusau.

 

Jagora: Muhammadu Ɗansanda .

‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka.

 

  Jagora: Ladan GilbaɗI nag ode mai,

‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka,

 

  Jagora: Shi ladan Gilbaɗi ya kyauta man,

‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka.

 

  Jagora: Alhaji Adamu Abubakar.

  ‘Y/ Amshi: Ya yi man bajinta don mi ya taimaka,

 

 Jagora: Isah Direba na gode mai.

 ‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka

 

 Jagora: Amadu Zurmi ina gode mai.

 ‘Y/ Amshi: Darajjam malan ya taimaka.

: E.O,

: Audi Baturen gona Allah yai ma rabo.

 

Jagora: Godiya Amadu Jabo.

‘Y/ Amshi: Ya yi man bajinta don mi ya taimaka.

 

 Jagora: E. O. 

‘Y/ Amshi: Alhaji Audi Baturen gona,

: Allah yai ma rabo.

 

Jagora: Ma’aikatad da an nan kowace ta anka yo.

: Ta san Gwamnati gona garat[2].

‘Y/ Amshi: Su ka abinci kullun a ci.

 

 Jagora: Sa’ad da hatci na tcada ƙwarai.

: Da kwanon dawa yah hamɓare.

‘Y/ Amshi: Gwamnati gona ta yi ƙoƙari.

: Da tas sa hannu ta taimaka.

 

Jagora: Turawa duka ko sun gamu,

: Baturen gona shi ag gaba,

: Shi ka biɗam maku rayis.

‘Y/ Amshi: Tare da ƙwai mai kyawo kullun a ci.

 

Jagora: Ka ga Turawan gona,

 ‘Y/ Amshi: Su sunka ɗara kowa ilmi na tabbata.

 

 Jagora: Kuma matan gona.

‘Y/ Amshi: Su sunka ɗara mata kyawo na tabbata.

 

 Jagora: Ka ga matan gona daidai da su,

: Sun sha rayis sun ɓakuce[3].x2

 ‘Y/ Amshi: Kowace nono ya yo tsaye,x2

 

 Jagora: Ka ga bayan nono ya yo tsaye,x2

  ‘Y/ Amshi: Jiki yai kyawo ya mulmule.x2

 

 Jagora: Habiba Balarabe Yabbuga Yawuri,

: A’i Aleru da sauransu duk.

: Wasila E.S ke ag gaba.x2

‘Y/ Amshi: Kun ɗara mataye arziki,x2

 

 Jagora: Baturen lambu ya hi baturen taba,

: Ko yau na tabbata,

: Zaman na tai lambu.

‘Y/ Amshi: Munka sha kashuna gwaiba sai mun gaji.

 

 Jagora: Baturen lambu ya hi baturen taba,

: Ko yau na tabbata.

: In an ce a aje su a zaɓa,

: Me kaka zaɓi kai mallami.

‘Y/ Amshi: Lemun zaƙi shi nika ɗauka,

: Kunnen taba ɗwaci garai.

 

 Jagora: Akwai tabako ya sha hura da nono,

: Ni iske ya bugu,

: Yam mance kwalin.

‘Y/ Amshi: Godilan[4] da bensin na tcinta munka yas.

 

 Jagora: Ku ban noma taba.

‘Y/ Amshi: Maza ku noma gero, dawa ko auduga.

 

 Jagora: Ƙabila kowace ta.

‘Y/ Amshi: Bata walwala ga yunwa na tabbata.

 

Jagora: Kullun manya gargaɗi sukai.x2

‘Y/ Amshi: Ku zan tsare aiki shi ab batu.x2

 Jagora: Ai da munka biyo mun ishe gandun gyaɗa,

: Mota ɗarid a goma shabakwai.

‘Y/ Amshi: Gyaɗa tai kyawo ta kammale.

: Ko can aiki shi yat tsara,

: Audi baturen gonag Gusau.

 

Jagora: Alhaji Audi na Alhaji Bunu.

‘Y/ Amshi: Wahabu ya hore ma zamani.

 

Jagora: Karo da giwa baya daɗi na Sanda.

‘Y/ Amshi: Kun sa kari ya sha wuya.

 

 Jagora: Kyawon kutsawa zarcewa.

  ‘Y/ Amshi: Wani ya kutsa ya sargahe[5].

 

 Jagora: Wane kare mai ƙaryat tciya,

: Baƙin tunku mai garjen tciya.

‘Y/ Amshi: Wahabu ya ɓata ma lokaci.

 

 Jagora: Wane kare mai kashin tsaki,

: Baƙin tunku mai garjen tciya.

‘Y/ Amshi: Wahabu ya ɓata ma lokaci.

: Ko can aiki shi yat tsara,

: Audi baturen gonag Gusau.

 

Jagora: Na Adamu Wara na Garba Ciwada.

 ‘Y/ Amshi: Darajjar malan ya taimaka.[1]  Saboda wane.

[2]  Gareta/ take da ita. Wato ta mallaki gona.

[3]  Ƙiba saboda jin daɗi.

[4]  Sunan taba sigari ne, wato “Goldleaf”

[5]  Kamar ka je wucewa wata hanya sai wani abu ya riƙe maka riga har ka kasa wucewa.

Post a Comment

0 Comments