Ticker

6/recent/ticker-posts

Kamancen Fifiko

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Kamancen Fifiko

Wannan ita ce kamantawar da mawaƙi kan yi amfani da ita a tsakanin wasu abubuwa biyu amma ya nuna duk da yake suna da kama da juna ɗaya daga cikinsu ya ɗara ɗayan wannan kamar. Wato a fifita ɗaya a kan ɗaya ta fuskar abin da ake so mai saurare ya kalla. Ana amfani da kalmomi kamar su wane, ya fi, ya zarce, babu awa, babu kamar da sauran irinsu wajen aiwatar da irin wannan kamance. Ga misali:

 Jagora: Kanta ƙwaƙwal, ƙwaƙwal kamab babu gashi,

Amshi: To

Jagora: Ko guiwar amali ta fi shi manga.

 (Waƙar Ƙazama : Inno mai bara Sabuwar hanya)

A wannan ɗan waƙa mai waƙar ya kamanta kan ƙazamar mace da gwiwar raƙumi amali wajen rashin gashi kuma har gwiwar ta amali ta fi kan ƙazamar mace gashi. Mawaƙin na son a dubi kan ƙazamar mace a kwalɗe kamar yadda gwaiwar amalin raƙumi tare da fifita yawan gashin da ke akwai ga gwiwar ta amali(idan akwai shi) bisa ga wanda ke akwai ga kan ƙazamar mace.


Post a Comment

0 Comments