Ticker

6/recent/ticker-posts

Kamancen Daidaito

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Kamancen Daidaito

Wannan ita ce kamantawar da mawaƙi kan yi tsakanin abubuwa biyu domin nuna daidaitonsu ga abin da yake nufi. Akwai irin wannan salo da yawa a cikin waƙoƙin bara. Misali:

Landi landi landiya,

Ɗan yaro bai sha ba ne,

Ni han na sha na rage,

Ɗanƙane yas shanye mani,

Ɗanƙane mai kurtun ciki,

Ciki kamar ƙundun Duwa,

 (Landiyo)

A wannan waƙar a layi na ƙarshe akwai salon kamance a inda aka ya kamanta cikin Ɗanƙane da ƙundun Duwa (wani ƙaton ƙololo ne da ya fito ga marar wani mahaukaci da ake kira Duwa). A nan mai waƙar na son mai saurarensa ya dubi cikin Ɗanƙane da idanun zuciyarsa kamar yadda ya san yana ganin ƙundun nan da aka san Duwa da shi. A nan an yi amfani kalmar kamance ‘Kamar’ domin daidaita girman cikin Ɗanƙane da ƙundun Duwa. Ga alama mai baran ya kawo labarin wani abin sha ne wanda ya raga ya ɓoye wa kansa amma sai Ɗanƙane ya gane kuma ya shanye. A ƙarshe sai ya zolaye shi ta hanyar kamanta cikinsa da ƙundun da aka san Duwa da shi.


Post a Comment

0 Comments