Ticker

6/recent/ticker-posts

Kamancen Kashi Ko Gazawa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Kamancen Kashi Ko Gazawa

Wannan ita ce kamantawa da mawaƙi kan yi amfani da ita a tsakanin wasu abubuwa biyu amma ya nuna ɗaya bai kai ga ɗayan ba ta fuskar kamar da yake son mai saurarensa ya ɗauka akwai ta tsakanin waɗanna abubuwa biyu. Ana amfani da kalmomi irin su bai kai, ko bai yi, ya kasa da sauran irin waɗannan. Misali:

Ya Ilahil Arshi, ba ni,

Hankali da yawan bayani,

‘Yan’uwa suka tambaye ni,

Mui ma waƙar tamu sani,

Gyara ba zai kamar kashi ba.

 (Aliyu Namangi: Imfiraji)

A wannan waƙar akwai kamancen kasawa a cikinta a ɗango na biyar, a inda aka kwatanta gyara da kuma kashi a sama, akwai kamantawa ta kashi a ciki – Gyara ba zai kamar kashi ba. Wannan na nufin gyara ya kasa don bai kai ga kashi ba wato wata waƙar da mawaƙin zai yi a matsayin gyara ba za ta kai ga ta farko da ya riga ya yi ba, duba a layi na biyar a sama.


Post a Comment

0 Comments