Ticker

6/recent/ticker-posts

Jinsintarwa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Jinsintarwa

Jinsintarwa dabara ce inda akan yi kwatancen ta fuskar jinsi wato a ɗauki halayyar wani jinsi a ba wani jinsin daban. Ɗangambo, (2007:45).

Jinsi shi ne iri, wato irin wni abu kamar halitta wanda ya bambanta shi da sauran irinsa. Misali jinsin mutum ko jinsin dabba da dai sauransu. A jinsantarwa ana ɗaukar halayya ko ɗabi’ar wani jinsi a saka wa wani jinsi da ba a san shi da irin wannan halayya ko ɗabi’a ba. Ana irin wannan ne domin ɗaukakawa ko ƙasƙantawa gwargwadon manufar mawaƙi. Akwai jinsi iri-iri da ya haɗa da na mutum ko dabba ko ƙwari ko tsirrai da sauransu. Masu nazarin adabi suna amfani da salo iri uku na jinsantarw; wato mutuntarwa da dabbantarwa da abuntarwa.

Post a Comment

0 Comments