Ticker

6/recent/ticker-posts

Mutuntarwa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Mutuntarwa

Mutuntarwa tana nufin Mawaƙi ya ɗauki wata halayya ko ɗabi’a ta mutum ya saka wa wani abu da ba mutum ba kamar dabba ko tsauni ko ƙwaro da sauransu, kuma ya kasance wannan halayyayr ko ɗabi’ar mutum ne kawainaka san shi da ita. To amma wani lokacin abin yakan zama akasin haka, Ɗangambo (2007:45). Misali:

 “Kura ta ga ɗan bara ɗan almajiri,

Bari in bi ka ɗan bara ko in san gari,

Tafiyata da taki ba ta zama ɗai da ɗai,

Ke ƙwace kikai ga mata ba su ba ki ba,

Ni roƙo nikai ga mata ‘yan arziki,

(Ya Tabaraka ya Rabbana)

A layi na biyu na waƙar da ta gabata an nuna almajiri yana zance da kura, ya faɗi ta faɗi. Ta ce za ta bi shi su shiga gari amma ya ce a’a, ya kuma gaya mata dalilansa na ƙiyawa. A nan an nuna kura na magana tamkar yadda mutum ke yi kuma tana fahimta maganar mutum idan ya yi. Yin magana da fahimtar ma’anar da ke ƙunshe cikin zance duka ɗabi’u da halaye ne na mutum amma aka ɗora su ga kura wadda take dabba. To a nan an mutuntar da kura, wato an saka mata halaye da ɗabi’u irin na mutum.

A wani misalin daga wata waƙar cewa ake:

Kogon kura na shiga,

Ko na damisa na shiga,

Sai tat taso man tsaye,

Sai nic ce wa zaki ci,

Sai tac ce mai magani,

Sai na baɗe ta da magani,

Kahin a jima ban gan ta ba.

(Karatun Magani)

A wannan waƙar mai suna karatun magani da almajiran ke bara da ita akwai mutuntarwa. An nuna mai shiga kogo ya haɗu da damisa har sun yi sa-in sa da juna. Wannan ka ce- na ce da ya shiga tsakani damisa da mai ɗibar magani halayya ce da aka san mutane da ita, amma sai ga shi ga damisa. To ke nan an mutuntar da damisa an ce tana magana yadda mutum yake yi.

Duk da yake salon jinsantarwa kashi uku ne kamar yadda bayani ya gabata, kashi ɗaya ne kawi aka iya samo misalansa daga cikin waƙoƙin bara da na sami kaiwa gare su. Sauran kasusuwan biyu, wato dabbantarwa da abantarwa ba a sami misalansu ba.


Post a Comment

0 Comments