Ticker

6/recent/ticker-posts

Haruna Dan Mani (Sarkin Noman Mayanci)

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Haruna Dan Mani (Sarkin Noman Mayanci)

 

G/Waƙa : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : Haruna Ɗan Mani,

: Barkar ka da ya kin kai,

: Tausar yama,

: Ga wag ga ƙasa duk mai riƙe kalme,

: Ya san da kai.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : Ga Ladan ga Karto tare da Ada na dangi,

: Sai sun zo aiki ya ka ƙarewa,

: Nan da nan,

: Tunda sai sun zo aiki ya ka ƙarewa,

: Nan da nan.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora  : Tunda sabra ba ta buwaya,

: In sun ka zo,

: Saboda na san samra ba ta buwaya,

: In sun ka zo.

 ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : To ai ko can ‘yan yara,

: Ka katsewa don wuya.

‘Y/Amshi : Arna bakin rai suka aiki,

: In sun ka zo,

: Aiki in kuma bai ƙare ba,

: Su sha ‘Billahillazi,

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

 Jagora: Himma na Abu,

: Kai ma ni kyauta daidai da ni,

: Ni kuma in shirya maka waƙa,

: Dai-dai da kai.x2

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : Ɗan Mani ka gaji bajinta,

: Wajjen uwa,

: Ɗan Mani ka ga ji bajinta,

: Wajjen uba.

: Kai Ɗan Mani ka ga ji bajinta,

: Wajjen uwa,

: Ɗan Mani ka gaji bajinta,

: Wajjen uba.

: To ni kuma ba raggon makaɗi,

: Nah haihoni ba.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora  : Yanzu Mayanci,

: Can aka sabga[1] ta ƙwarai,

: Abin da duk nir roƙa,

: Ba a cewa babu shi,

: Audu bara na saki da su,

: Na zo in shaida maka,

: Yunwar tsaba garan,

: Na zo in shaida maka,

: Yunwar kuɗɗi garan,

: Tamkar jariri nike,

: Ni ban san babu ba.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : Abu Tafidan Zurmi,

: Tare da Sarkin Noma,

: Haruna ban yi musun,

: In samu kujera wajjensu ba.

‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : Garba Abu Daura,

: Ɗan Alhajiya shiryayyen mutum,

: Garba Abu Dauran, 

: Ɗan Alhajiya shiryayyen mutum.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

 Jagora : Haruna Ɗan Mani,

‘Y/Amshi : Barkar ka da yaƙin tausar yama,

: Ga wag ga ƙasa,

: Duk mai riƙa kalme,

: Ya san da kai.

 

 Jagora : Audu na aje roƙo gidan ka,

: Gidan katanga mi ag ga rai?

  ‘Y/Amshi: Wajjen mai miƙa muna samu,

: Can munka yi,

: Mijin Jaɓɓo da Hauwa da Inno,

: Cikakken mutum,

: Allah bai yo Alhaji,

: Samnan[2] dattijo ba,

: Wahabu Allah bai yo Alhaji,

: Samnan dattijo ba,

 

Jagora : Imani ya kammala,

: Guri nai ya cika,

: Kamar ya je aikin hajji,

: Ya samu gida Gusau.

 ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : Tunau Cika Hanna,

: Babba na Alhaji Sabon gari,

: Mai nasarar damana,

: Mijin Jaɓɓo na dan hababba,

: Na tuba duk banga mutum,

: Mai nomanka ba,

: Ƙasar ga na duba duk,

: Banga mutum mai nomanka ba.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona yakwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

Jagora : Kiɗin da niy yi ma,

: Ga rediyo nika kai,

: Amma sai jama’a,

: Sun ce mani waƙar nan ta shiga,

: Kiɗin da niy yi ma,

: Ga rediyo nika kai,

: Amma sai jama’a,

: Sun ce mani waƙar nan ta shiga.

: Mijin Inno ka yi man wasiƙa,

: Ta kai ga ran,

: Na san alheri muka samu,

: In munka zo.

 

  Jagora  : Mijin Jaɓɓo da kay yi man wasiƙa,

: Ta kai garan,

 ‘Y/Amshi : Na san alheri muka samu,

: In mun ka zo.

 

  Jagora  : Mai gidan Kuluwa ka yi man wasiƙa,

: Ta kai garan.

  ‘Y/Amshi: Na san alheri muka samu in munka zo,

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

Jagora : Gabas ga Mayanci,

: Ba su da daji ko ɗan kaɗan,

: Sarkin noman yamma,

: Ga kwalta ya sassabe,

: Gabas ga Mayanci,

: Ba su da daji ko ɗan kaɗan,

: Sarkin noman yamma,

: Ga kwalta ya sassabe[3],

 

 Jagora: To in dai niz zo Mayanci,

: In zo da mayaya niyo,

: Sai na tahi na gano,

: Bahillacen arziki,

: Ni dai ban rena ma muhaman, 

: Ɗan zainaba ba.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora: Haruna Ɗan Mani,

: Barkar ka da yaƙin,

: Tausar yama,

‘Y/Amshi : Ga wag ga ƙasa,

: Duk mai riƙe kalme,

: Ya san da kai.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora: Haruna Ɗan Mani,

  ‘Y/Amshi: Barkar ka da yaƙin,

: Tausar yama.

: Ga wag ga ƙasa,

: Duk mai rike kalme,

: Ya san da kai.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

 Jagora: Ɗan Mani barkak ka da yaƙin,

: Tausar yama,

: Ɗan Mani barkak ka da yaƙin,

: Noman hatsi,

: Dan Mani,

: Barkak ka da yaƙin,

: Noman gyaɗa.

  ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora: Haruna Ɗan Mani,

‘Y/Amshi: Barkar ka da yaƙin,

: Tausar yama,

: Ga wag ga ƙasa,

: Duk mai riƙe kalme,

: Ya san da kai.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu,

 

  Jagora: Ya nuna min Isa,

: Jikan Jatau halin bajinta,

: Shi ya yi man,

: Zaman[4] ya ba,

: Audun Baraka,

: Kyautar goɗiya[5].

 

Jagora: Ɗan Masanin Bunguɗu, 

: Mijin Hajiya Rabi,

: Mijin Hajiya Hafsi,

: Mijin Hajiya Hasiya,

 ‘Y/Amshi : Ni dai ban re na ba,

: Da halin girmanka ba,

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora: Haruna Ɗan Mani,

: Barkar ka  da yaƙin,

:Tausar yama.

‘Y/Amshi: Ga wag ga ƙasa,

: Duk mai riƙa kalme,

: Ya san da kai.

 

  Jagora: Ɗanmasanin Bunguɗu,

: Mijin Hajiya Rabi,

: Mijin Hajiya Hafsi,

: Mijin Hajiya Hasiya,

: Mijin Hajiya hasiya,

  ‘Y/Amshi : Ni dai ban rena ba,

: Da halin girmanka ba,

: Don ko ka taimaka,

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona yakwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora: Haruna Dan Mani,

: Barkar ka da yaƙin,

: Tausar yama,

‘Y/Amshi: Ga wag ga ƙasa,

: Duk mai riƙe kalme,

: Ya san da kai,

 

 Jagora: Mijin Jaɓɓo da kay yi min wasiƙa,

: Ta kai garan,

  ‘Y/Amshi : Nasan alheri muka sa mu,

: In mun ka zo,

 

Jagora : Mai gidan Inno,

: Ka yi min wasiƙa,

: Ta kai garan.

 ‘Y/Amshi  : Na san alheri muka samu,

: In mun ka zo.

 

Jagora: Mai gidan Kuluwa,

: Ka yi min wasiƙa,

: Ta kai garan.

 ‘Y/Amshi  : Na san alheri muka samu,

: In mun ka zo.

: To in dai ba ka miƙa mana,

: Damman geronka ba,

: Ka na da halin miƙa,

: Muna damman wazobiya[6].

‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora: To shi dai raggo,

: Ba ya buƙatar komi garan,

: To shi dai raggo,

: Ba ya bukatar komi garan,

‘Y/Amshi: Gaya mai ko ni,

: Ba ni buƙatar komi garai.

 

  Jagora: Tunda daga mazan kirki,

  ‘Y/Amshi : Mis sa mu biyas,

: Shaggun gorina.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

  Jagora : Gidan mutumin kirki,

: Aka samun sabgar[7] ƙwarai,

: Gidan raggo sai masu,

  ‘Y/Amshi: Sai masu shiririta ar akwai.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona yakwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora : Ya nuna min isa,

: Jikan Jatau halin bajinta,

: Shi yay yi min,

: Zaman ya ba Audun Baraka,

: Ka ban goɗiya[8],

: Baban su Kabiru,

: Yanzu miƙa min raƙumi,

  ‘Y/Amshi: Mu nemi akala[9] in riƙa,

: Ɗaukar kaya da shi.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu,

 

  Jagora  : Randa yay yi Noma,

: Yas samu abinci nai ya isai,

: Gidan raggo ko yaushe,

: Abinci  ya bar isa,

: Shi dai raggo babu hatsi,

: Ba kuɗin saye,

: Matanai sun firgita,

: Sun ce duk sun hita,

 ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

 Jagora  : To shi dai rag go ,

: Babu hatsi ba kuɗɗin saye,

: Matanai sun firgita,

: Sun ce duk sun fita,

: Agaji raggo tun yinwar ga,

: Danye ya ci,

: Bagudu don Allah,

: Ɗan ‘yam mashi rogo,

: Ɗanye ya ci,

: Ya ɗau kwashe,

: Za ya ginar sanyun kirshiya,

: Da yay noma yaɗ ɗebe,

: Ƙalilan yag gurgura,

 ‘Y/Amshi : Sai yac ce sayenta,

: Ashe ƙaiƙai  ag garai.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

Jagora: Ran batun ilimin nan,

: Za’a biɗar babban malami,

: Wurin Noma nan za’a biɗam,

: Mai ƙarfi ya zo.

 ‘Y/Amshi : Mu kama kiɗi,

: Mu kam haka Allah,

: Yay yo da mu.

 

Jagora  : Kai mu kama kiɗi,

‘Y/Amshi : Mu kan haka Allah,

: Yay yo da mu.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

  Jagora  : Ɗan Mani ka gaji bajinta,

: Wajen uwa,

: Ni kuma ba samnan, 

  ‘Y/Amshi: Makaɗi nah haihoni ba,

 

Jagora : Na gode Adamu Abdullahi Kanoma,

: Dogo ba’a canye ka ga,

: Aikin radiyo ba.

  ‘Y/ Amshi: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

 Jagora: To na aje roƙo gidan,

: Bahili[10] mi ag garai?

: Garkar mai miƙa mini

: In ba ni

: To na aje roƙo gidan

: Bajinta mi ag garai

: Garkar mai miƙa mini

: Can munka yi.

‘Y/Amshi: Sarkin Noma

: Mai hana aikin gona Ya kwan

: Matsa a gama manya

: Makasa sabra Ɗan Abu

 

  Jagora: Na Magajin Gari,

: Mijin Jaɓɓo,

: Da Inno da Hauwa cikakken mutum,

: Allah bai yo Alhaji,

 ‘Y/Amshi : Samnan dattijo ba,

: Wahabu Allah bai yo Alhaji,

: Samnan dattijo ba.

 

 Jagora: Imani ya kamala,

: Guri na ya cika,

: Kamar ya je sallah,

: Haji ya samu gida Gusau.

‘Y/Amshi: Wuri shidda garai,

: Kowa ne kau ba ɗan tsito[11] ba,

: Kowa ne wuri an ɗebi,

: Buhun shinkafa ɗari,

: Wanga guri an ɗebi,

: Buhun shinkafa ɗari,

: Ni na san mota,

: Aka ɗaukar ranar jida.

  ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona yakwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

 Jagora: Gabas da Mayanci,

: Ba su da daji ko dan kaɗan,

 ‘Y/Amshi  : Sarkin Noman yamma,

: Ga kwalta ya sassabe.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona yakwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

 Jagora: Da ya noma hatsi nai,

: Ya fitar da haƙƙin[12] Rabbana,

: Ba ya barin sai masu bidar,

: Zakka sun  matsu.

 ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu,

 

 Jagora: Da ya darme hatsi nai,

: Ya fit da hakin Rabbana,

: Ba ya barin sai masu biɗar,

: Zakka sun matsu,

: Ya nuna man Isa,

: Jikan Jatau halin bajin ta,

: Shi yay yi man,

: Zaman ya ba Audun,

: Baraka kyautar goɗiya.

 ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

 Jagora: Ginjimin Tukur ka ban goɗiya,

: Baban su Kabiru,

: Sake miƙa man Raƙumi,

: Na nemi akala,

: In riƙa ɗaukar kaya da shi.

 ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.

 

Jagora: Haruna Ɗan Mani,

  ‘Y/Amshi: Barkak ka da yaƙin,

: Tausar yama,

: Ga wag ga ƙasa dum,

: Mai riƙa kalme,

: Ya san da kai.

: Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra[13] Ɗan Abu.

 

  Jagora: Mijin Jaɓɓo da kay yi man wasiƙa,

: Ta kai garan.

: Na san alheri muka samu,

: In mun ka zo.

: Mai gidan Inno ka yi min wasiƙa,

: Ta kai garan,

: Na san alheri muka samu,

: In mun ka zo.

‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

: Mai hana aikin gona ya kwan,

: Matsa a gama manya,

: Makasa sabra Ɗan Abu.



[1]  Hidima/Sha’ani.

[2]  Saunan mutun wato raggo wanda bai iya noma abincinsa.

[3]  Sare ‘yan itatuwa da ciyayi domin a gyara gona don noma.

[4]  Saboda.

[5]  Matashiyar macen doki.

[6]  Kuɗi.

[7]  Halayya.

[8]  Maccen doki.

[9]  Igiyar da ake ɗaura wa raƙumi ana ja.

[10]  Raggo

[11]  Kaɗan

[12]  Zakka.

[13]  Wurin da ba a noma ba wanda hakukuwa suka fito daba-daban.


Post a Comment

0 Comments