Ticker

6/recent/ticker-posts

Jikan Dan Amadu Bajini

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Jikan Ɗan Amadu Bajini

 

 G/Waƙa: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

: Mai ganga ya zaka,

: Ya ganai.

 

  Jagora: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

: Mai ganga ya zaka,

: Ya ganai.

  ‘Y/Amshi: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

: Mai ganga ya zaka,

: Ya ganai.

 Jagora: Ɗan Daudu magajin Ɗansani,

‘Y/Amshi: Ɗan Daudu magajin Ɗansani,

: Bai yadda ya zanna birni ba,

: Mai kalmen kashe gazama[1].

: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

: Mai ganga ya zaka,

: Ya ganai,

 

  Jagora : Ƙwairo,

‘Y/ Amshi: Ya yadda da  Bajini,

 

  Jagora: Mamman,

 ‘Y/Amshi: Ya yadda da Bajini.

 

  Jagora: Haz Zaƙi,

‘Y/Amshi: Ya yadda da Bajini,

 

  Jagora: Sallak kwana.

‘Y/ Amshi: Ya yadda da Bajini.

 

  Jagora: Ali,

 ‘Y/Amshi: Ya yadda da Bajini.

 

Jagora: Dodo,

 ‘Y/Amshi: Ya yadda da Bajini,

 

  Jagora: Sai ga ‘yammata,

: Suna hwaɗin,

‘Y/Amshi: Ko mumun yadda,

: Da Bajini,

: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

 

  Jagora: Ya aje gero ga dawa,

: Ya yi gandun rakke,

: Ya yi gandun gujiya,

: Kuma ya yi gandun rakke,

: Rakkenai ta yi kyau,

‘Y/Amshi: An saisat[2] jikka tara da huɗu.

: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

: Mai ganga ya zaka,

: Ya ganai,

 

 Jagora: Mai saida dare ƙanen Musa,,

‘Y/Amshi: Gwarzon Sadi mai makwaso,

: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

 

Jagora: Ku zan tsare nomad a gaskiya,

: Ku bar yarda harkar banza,

: In dan goge sai an ƙoshi,

: Sai an ci tuwo aka yin banjo,

‘Y/Amshi: Sannan Mashal yake da ƙawa,

 

Jagora: In dai ya karɓi tuwon gero,

‘Y/Amshi: Sai ka gay a ƙuma zanzaro,

: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

: Mai ganga ya zaka,

: Ya ganai,

 

  Jagora: Sai ku ko ‘yanmatan Wurno,

: Ga waƙa nan na shira[3].

‘Y/ Amshi: In na gina maku ku iyat,

: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

: Mai ganga ya zaka,

: Ya ganai,

 

 Jagora: Mai saida dare ƙanen Musa,,

‘Y/Amshi: Gwarzon Sadi mai makwaso,

: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

 

 Jagora: Ba Barundayen banza ne ba,

: Tun da jijjihi yattai gona.

: Darzaza Ɗan Ubandawaki,

‘Y/Amshi: Allah yai maka ƙoƙari.x2

: Jikan Ɗan Amadu,

: Bajini,

: Mai ganga ya zaka,

: Ya ganai,



[1]  Wata ciyawa ce mai saye nisa a cikin ƙasa, sai babbar fartanya ke gino shi.

[2]  Sayar da ita.

[3]  Shiryawa.

Post a Comment

0 Comments