Ticker

6/recent/ticker-posts

Jibo Mai Ruwan Gabas

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Jibo Mai Ruwan Gabas

  G/Waƙa: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago[1],

: Ya nome ta.

 

Jagora: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

  ‘Y/ Amshi: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

  Jagora: Sai dare ƙanen Ba’u.

‘Y/ Amshi: Mijin Ba’u ne,

: Mijin ƙwairon ganga.

 

  Jagora: Ƙwairo ko miji,

:Ya ji daɗin aure.

‘Y/ Amshi: Ai ba ya ce ma matatai Inna.

 

  Jagora: In mace bata son ka,

: Kai kac ce ka so ta,

: Gwadin saiɓi[2] kenan,

: Sai ta sa ka suma.

‘Y/ Amshi: Kana ta raki

: Tana hwaɗin na rena ka.

: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

  Jagora: Ta Bunu ɗanki yai doki,

: Ki yi guɗa.

‘Y/ Amshi: Ki kau aza man,

: Sirdina.

 

Jagora: Damu ki bada kahu.

‘Y/ Amshi: Ham mai ƙarhi yana licin kawo,

 

  Jagora: Hassi da a uwaɗ ɗa.

‘Y/ Amshi: Bada jalala[3] takai,

: Sabo licin[4] ƙauna.

: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

 Jagora: Mai zwarin[5] wuri magajin.

‘Y/ Amshi: Malam mai zwarin wuri,

: Magajin Ɗanhawwa.

: Bai tsaya gida ba,

 

  Jagora: A gaida jibo,

: Mai ruwan Gabas.

‘Y/ Amshi: Bardoki a gaida jibo,

: Mai ruwan Gabas,

: Na gode ma.

: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

  Jagora: Mai garaya da yas sha yunwa,

: Sai ya biya gidan Sodo,

: Sai yas sha hura ta gero,

: Ya ɗauko Garaya,

: Yana ta ta kiɗi,

: Barzan[6] barzan,

: Barzan barzan,

: Barzan zanzan,

: Barzan zan,

: Barzan bazan,

: Barzam barzan,

: Bazam barzam,

: Barzan barzan,

: Zarzan.

: Bazam bazam,

: Barzan barzan zarzan ,

: Dodon gina gije kanun gayya.

: Sodangi[7] ɗan waɗan Tungat tunku,

 ‘Y/ Amshi: Geronka ya yi kyau,

: Gwarzon Dango.

: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

Jagora: Kare mai kashe barewa,

: Ko mai kashe ɓauna,

: Gami da gwanki,

‘Y/ Amshi: Wannan sunanshi,

: Ya haye man su yanzu,

: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

 Jagora: Mai garaya da yah hole,

: Ya kama zahin mahalba,

: Su dai sai taƙamab baƙin taggo[8],

: Ga burtu kahe da kai,

: Ga  Allad dawwama.

 

 Jagora: Sai dare ƙanen Ba’u.

‘Y/ Amshi: Mijin Ba’u ne,

: Mijin ƙwairon ganga.

: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

  Jagora: Mai zwarin wuri magajin.

‘Y/ Amshi: Mamman,

: Mai zwarin wuri maga..,

: Jin Ɗanhawwa.

: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

  Jagora: A gaida Jibo,

: Mai ruwan Gabas.

‘Y/ Amshi: Bardoki a gaida Jibo,

: Mai ruwan Gabas,

: Na gode ma.

: Bai tsaya gida ba,

: Ya wa gona dirar kago,

: Ya nome ta.

 

  Jagora: Mai zwarin wuri magajin.

‘Y/ Amshi: Mamman mai zwarin wuri,

: Magajin Ɗanhawwa.



[1]  Ɗanbisa na ɗakin/jinka.

[2]  Maganganu maras makama.

[3]  Kaza yake nufi da wannan Kalmar.

[4]  Ina-nika-aza ga yaro wanda iyaye suke yi don nuna masa ƙauna. Wato su riƙa yi masa duk abin da yake so.

[5]  Haɗama/son ya samu shi kaɗai/handama da babakere.

[6]  Wato yadda garayar take amo ne ya sifanta.

[7]  Mai so da taimakon danginsa.

[8]  Riga/Taguwa.

Post a Comment

0 Comments