Ticker

6/recent/ticker-posts

Isuhu Direba

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Isuhu Direba

Isuhu wato Yusuf direba asalinsa mutumen garin Gatawa ne, amma dai a halin yanzu ya koma da zama a Sabonbirni ta cikin jihar Sakkwato,  A lokacin da Amali ya yi masa waƙa direban wata mota ne da ake kira DALTA buɗaɗɗiya wadda ake ɗaukar kaya da ita.  A wancan lokacin an ce babu wanda ya fi shi gudu da mota saboda ƙwarewarsa da tuƙin motar. Yana nan da ransa kuma yana sana’arsa ta tuƙin mota. Ga waƙar tasa kamar haka:

 

   G/Waka  : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

: Da lambobin gudu,

 

 Jagora: Da gudu ƙwarai da rashin gudu,

   : Radda kwana nac cika,

: Tahiya garin kewa[1]akai.

 ‘Y/Amshi: Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

: Da lambobin gudu,

   : Allah ya tsare da tsarewa,

: Tai ka gama da kowa lahiya.

 

 Jagora: Da gudu ƙwarai da rashin gudu,

   : In dai da kwana duniya,

: Ai ba a kwana lahira.

  ‘Y/Amshi: kuma radda kwana naccika,

: Tahiya garin kewa a kai.

 

 Jagora: Sai wataran da ku yan gasawa,

   : Tahiya gida na zani yi,

‘Y/Amshi: Tahiya gida na zani yi,

: Jama’ag ga sai kuma an jima.

 

Jagora  : In dai magana ta jan mota ce,

   : In dai magana ta cin hanya ce,

   : In dai magana ta jan ƙarhe ce,

   : Issuhu ya yi malin[2] kowa.

‘Y/Amshi: Ba mota ba sai jirgin sama,

   : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

: Da lambobin gudu,

   : Allah ya tsare da tsarewa,

: Tai ka gama da kowa lahiya.

 

   Jagora  : Wanga irin yaro da gaugawa kake,

‘Y/Amshi: Wanga irin yaro akwai sarmin[3] kwana,

 

   Jagora  : Wanga irin yaro akwai sarmin kwana.

‘Y/Amshi: Wanga irin yaro da gaugawa yake.

   

Jagora  : In ya kai wuri mai turɗa,

: Issuhu hihhikawa[4] za yai,

‘Y/Amshi: Ba ya aje ta sai in ya wuce,

   : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

: Da lambobin gudu,

  : Allah ya tsare da tsarewa

: Tai ka gama da kowa lahiya.

 

 Jagora  : Wani mai tebur da yaj ja gardama,

   : Shinkafi yaj ja gardama ,

   : Kuma zaya kai kaya Kano,

   : Issuhu ya shigo mota tai,

   : Shi ma za shi kai kaya Kano,

   : Yaro tsaya sai na wuce.

‘Y/Amshi: Shi ko yac ce Oga[5] ƙarya kakai,

 

Jagora: Dan Yaro tsaya sai na wuce,

‘Y/Amshi: Shi ko yac ce Oga shi ak kure,

 

 Jagora  : An ka zuba ta hilin godabe,

   : Mai tebur yana bisa titi,

   : Sai taya guda ɗai ta hwashe,

   : Bai daina ba sauri ɗai yakai.

‘Y/Amshi: Samri[6] ɗai yakai,

: Taya guda kuma ta hwashe,

 

 Jagora  : Mun ka wuce shi Ƙaura ya tsaya,

   : Ya raɓa Dauran yaw wuce ,

   : Yar raɓa Gurbi yaw wuce,

   : Bai tswalka[7] ba hay yak kai Kano,

   : Ummaru ya riƙe mashi hannu.

‘Y/Amshi: Don Allah tsaya ka kai Kano.

 

Jagora  : Sai dai munka dubi agogonai,

‘Y/Amshi: Minti biyar yaz zo Kano.

   : Da gaskiya ya kasa injin tahiya,

: Da lambobin giya,

   : Allah ya tsare da tsarewa,

: Tai ka gama da kowa lahiya.

 

Jagora  : Rannan na ishe shi yana hutawa,

   : Ya yi zanne cikin gida,

: Yac ce taho magana nikai.

   : Ni ko da nit tahi nib biya,

   : Ni ko da nittahi nib biya,

   : Ya ce ina maganak kiɗi?

   : Na ce akwai maganak kiɗi,

   : In dai sakin waƙa ne,

: Kan da bakwai guda ƙarya ni kai,

   : To kai ! ina maganar gudu?

   : Ya ce akwai maganar gudu,

   : Amali ko ka san awa ?

   : Na ce da shi na san awa.

 

 Jagora: In niy yi awa ban kai ba Kano,

: Ce ba ni bangon duniya.

    ‘Yan Amshi  : In niy yi awa ban kai ba Kano,

: Ce ba ni bango duniya.

  : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

: Da lambobin[8]gudu,

   : Allah ya tsare da tsarewa,

: Tai ka gama da kowa lahiya.

 

Jagora  : Mai hijo[9] sakam muna hili.

‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi ƙarya yakai.

 

Jagora: Mai datsun ɗaga muna kai ma.

‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi ƙarya ya kai.

 

 Jagora: Mai balbo ɗaga muna kai ma.

‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi ƙarya ya kai.

 

Jagora  : Mai sharido shi yam muna hili,

‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi ƙarya yakai.

 

 Jagora  : Har mai roka ya yam muna hili,

‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi ƙarya yakai.

 

Jagora  : Ku ji dinka[10] tana kumburi ga banza.

‘Y/Amshi: Mun ka wuce su bayan Moriki,

   : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

: Da lambobin gudu,

   : Allah ya tsare da tsarewa.

   : Tai ka gama da kowa lahiya.

 

Jagora  : Sai wataran da ku yan  Gatawa,

   : Tahiya gidana za ni yi.

‘Y/Amshi: Tahiya gidana za ni yi ,

   : Jama’ag ga sai kuma an jima,

   : Da gaskiya yaka sa mota tahiya

: Da lambobin gudu,

   : Allah ya tsare da tsarewa,

   : Tai ka gama da kowa lahiya.



[1]  Lahira.

[2]  Fi/tserewa, maganar fifiko ce.

[3]  Sauri /hanzari/Gaggawa.

[4]  Tashi sama.

[5]  Maigida.

[6]  Sauri/hanzari yin abu da gaggawa.

[7]  Wato bai sami wani ɓacin rai ba wanda ya sa shi ya yi tswaki.

[8]  Giyar mota kenan wato ta ɗaya har zuwa ta huɗu, ko ta biyar ko ma fiye ga waɗansu motocin.

[9]  Mota Fujo.

[10] Sunan wata mota ne wadda ake kira C.20 sai mutane suke kiranta kumburin Dinka.

Post a Comment

0 Comments