Ticker

6/recent/ticker-posts

Kammalawa - Daga Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Kammalawa

Komai ya yi farko zai yi ƙarshe in ban da ikon Allah, wannan aikin ya zo ƙarshensa a wannan lokaci, Allah ya ba da ikon ƙare aikin ne wanda a cikinsa ne aka binciki tarihi da waƙoƙin shahararren mawaƙin noman ne na wannan yanki na Yammacin Arew, wato jihohin Sakkwato da Kabi da Zamfara wanda kowa ya sani da suna Amali  Sububu. An dubi salsalar[1] mawaƙin sannan aka dubi yadda ya fara waƙoƙinsa da yadda suka bunƙasa a ƙasar Hausa bakiɗaya. An kuma yi tarken turakun waƙoƙin Amali  Sububu manya da ƙananansu. Bayan wannan an kawo waƙoƙin Amali  Sububu waɗanda ya yi wa manoma, da kuma waƙoƙinsa da ya yi wa waɗansu mutane waɗanda ba manoma ba, ko kuma a ce waƙoƙinsa da ya yi don noma da waɗanda ya yi ba don noma ba. An kuma bayar da wani ɗan taƙaitaccen bayani a kan mutanen da Amalin ya yi wa waƙar kafin a kawo kowace waƙar da ya yi masu, don a gane su kurum, a kuma san inda suka fito. Da fatar wannan aikin ya amfanar da jama’a musamman manazartan adabin Hausa.



[1]  Asalinsa.

Post a Comment

0 Comments