Ticker

6/recent/ticker-posts

Gwauro (Isihu)

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Gwauro (Isihu)

A garin  Sububu Isihu yake, ya daɗe bai da mata, kuma bai nuna damuwarsa ga rashin matar ba, har ma ya iya yin ayyukan da mata suke yi kamar hidimar abinci. Don haka sai Amali ya yi masa waƙar. Yana cikin yaran Amali masu yi masa amshi, kuma tare da shi aka yi masa waƙar. 

 

   G/Waƙa : Ya yi daren tuwo,

  : Bai samu gaban reda ba.

­

 Jagora: Ya yi daren tuwo,

: Bai samu gaban reda ba.

‘Y/Amshi: Ya yi rimis-rimis[1],

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Anne ya dahi cikin dutci,

‘Y/Amshi: Ya ce masu na kai kaka.

  : Ya yi rimis-rimis,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Gwauro ya samu cikin dutci,

: Yac ce masu na kakace,

‘Y/Amshi: Ya yi rimis-rimis,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Ya yi daren tuwo,

: Bai samu gaban dutci ba.

‘Y/Amshi: Ya yi rimis-rimis,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Maza reda,

: Maza reda,

: Kada tsabag  ga ta kai ɗan Ando,

‘Y/Amshi: Ya yi rimis rimis,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Hal linzami aka sa mai,

: In yak kata da reda.

: Sai an ja shi ya ɗan sassauta.

 

‘Y/Amshi: Ya yi ridin-ridin[2] ,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Hal linzami aka sa mai,

: In yak kata da reda,

: Sai an ja shi ya ɗan  sassauta.

‘Y/Amshi: Ya yi ridin-ridin,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Anne ya samu cikin dutci,

: Yac ce mana ya kai kaka.

‘Y/Amshi: Ya yi ridin-ridin,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Maza reda maza reda,

: Kada redag ga ta kai ‘yah hantci.

‘Y/Amshi: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Gwauro barkak ka da murzaƙ[3] ƙwaya.

‘Y/Amshi: Gwauro barkak ka da murzaƙ ƙwaya.

 

 Jagora: Gwauro barkak ka da ɓarzaƙ ƙwaya.

‘Y/Amshi: Gwauro barkak ka da muzaƙ ƙwaya.

  : Ya yi jirin-jirin ,

: Bai samu gaban reda[4] ba.

 

 Jagora: Maza reda maza reda,

: Kada tsabag ga,

‘Y/Amshi: Ta kai ma hantci,

  : Ya yi ridin-ridin,

:Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Ya yi daren tuwo,

‘Y/Amshi: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Anne ya samu cikin dutci,

‘Y/Amshi: Yac ce masa ya kai kaka.

 

 Jagora: Ya yi tuƙun-tuƙun,

: Bai samu gaban dutci ba.

‘Y/Amshi: Ya yi ridin-ridin,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Anne ya dahi cikin dutci[5].

: Yac ce ....

‘Y/Amshi: Yac ce mana ya kai kaka,

  : Ya yi ridin-ridin,

: Bai samu gaban reda ba.

 

 Jagora: Ya yi daren tuwo,

: Bai samu gaban reda ba.

‘Y/Amshi: Ya yi ridin-ridin,

: Bai samu gaban reda ba. x2

 

 Jagora: Ya yi daren tuwo.[1]  A daka hatsi su daku.

[2]  Wato mutum ya ɓata jikinsa da wani abu kamar gari.

[3]  Gurzar hatsi

[4]  Niƙa, wato gurzar hatsi a mayar das u gari.

[5]  Dutsen niƙa.

Post a Comment

0 Comments