Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Yi Rantsuwa Ba Zan Yi Wani Aiki Ba Sai Kuma Na Yi, Sai Na Yi Kaffara?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam rantsuwa na yi ba zan yi ma wata magana ba saboda ta zage ni, to na yi rashin lafiya sai ta je ganina, yanzun ta haihu da na ce bazan mata barka ba, to idan na je na yi mata magana sai na yi azumin kaffara guda ukku ko?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, E, haka ne za ki yi kaffara, amma abin da aka ce a fara yi shi ne, ciyar da talakawa guda goma (10) abinci, ko tufatar da su, ko ƴanta wuya (baiwa), idan mutum ba shi da hali ne sai ya yi azumi uku, kamar yadda aya ta 89 da ke Suratul Ma'ida ta tabbatar:

لَا يُؤَاخِذُكُمُ اللَّهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ وَلَٰكِنْ يُؤَاخِذُكُمْ بِمَا عَقَّدْتُمُ الْأَيْمَانَ ۖ فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ ۖ فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ ۚ ذَٰلِكَ كَفَّارَةُ أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ ۚ وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa ´yantãwar wuya. Sa'anan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. Wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa. (Suratul-Má'ida 89)

Kuma ciyarwar ba dole sai a rana ɗaya ba, mutum zai iya kullum ya ciyar da miskini ɗaya har na kwana goma. Kuma don Allah ki je ki yi mata barka ɗin kada ki fasa saboda wannan ciyarwar ko azumin, don Allah ki je ƴar uwa.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments