𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As Salaamu Alaikum. Miji ne ba ya bai wa matarsa
haƙƙinta na zamantakewa, kamar sakin fuska da hira da bayar da abinci da ɗinka sutura da sauran kayan masarufi irin
yadda yake bai wa kishiyarta, wai dole sai ta amince da abin da yake so, wai
sai ta yarda a riƙa yi mata allurar rage haihuwa! Meye hukuncin
wannan a shari’a?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
[1] Da farko ya kamata duk mu san cewa: Haihuwa
baiwa ce kuma kyauta ce daga Allaah Mabuwayin Sarki, yana bayar da ita ga wanda
yake so, a sadda, da inda, kuma ta yadda yake so, kamar yadda ya faɗa a cikin Suratu Shuura:
لِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ ، يَهَبُ لِمَنْ يَشَآءُ إِنَاثًا وَيَهَبُ لِمَنْ يَشَآءُ الذُّكُورَ ، أَوْ يُزَوِّجُهُمْ ذُكْرَانًا وَإِنَاثًا ، وَيَجْعَلُ مَنْ يَشَآءُ عَقِيمًا ، إِنَّهُ عَلِيمٌ قَدِير
Mulkin sammai da ƙasa na Allaah ne kaɗai, yana halitta duk abin da ya ga dama,
yana yin baiwar ’ya’ya mata ga wanda ya ga dama, kuma yana yin baiwar ’ya’ya
maza ga wanda ya ga dama, ko kuma ya gauraya su maza da mata (ga wanda ya ga
dama), kuma yana ƙyale wanda ya ga dama a matsayin bakarare, haƙiƙa shi mai
ɗimbin sani ne, mai
cikakken iko.
A yau kuwa muna ji da ganin yadda ma’aurata da
yawa suke neman haihuwar maza da mata a haɗe, ko irin nau’in da bai ba su ba amma
kuma ba su samu ba, kamar kuma yadda muka sha ji da ganin waɗanda suke ta ƙoƙari rani da damina,
ba-dare ba-rana don samun ko da haihuwar sau ɗaya ma, amma dayake Mai Yin Baiwar bai
bayar ba, dole suka yi haƙuri suka dangana. Sannan kuma a kullum mana ji da
ganin yadda ma’aurata
suke murna da farin ciki a duk lokacin da Mabuwayin Sarki Mai Yawan Baiwa ya
albarkace su da samun haihuwa. Waɗannan
abubuwa ne sanannu tabbatattu a cikin musulmi da kafirai da dukkan al’ummomin
duniya.
[2] Ni’imomin da Ubangiji Ta’aala ya yi wa bayinsa
a koyaushe suna da yawan gaske, kamar yadda ya faɗa a cikin Suratun Nahl:
وَإِنْ تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللَّهِ لَا تُحْصُوهَا إِنَّ اللَّهَ لَغَفُورٌ رَحِيمٌ
Kuma in da za ku lissafe ni’imomin Allaah a gare
ku, ba za ku iya ƙididdige su ba, lallai Allaah tabbas! Mai Yawan Gafara
ne, Mai Yawan Rahama ne.
Sai dai kuma duk da hakan ba mu taɓa ko jin labarin wani mutum guda ɗaya mai hankali da tunani ba ya taɓa ƙyamatar ko da mafi ƙanƙantar baiwa guda daga
cikin ɗimbin
ni’imomin Ubangiji Ta’aala ba a gare shi. Babu wanda ya taɓa ƙyama ko jin haushi idan itatuwan mangwaro
ko lemu ko ayaba a gonarsa suka fitar da ’ya’ya
masu yawan da bai taɓa
ganin irinsu ba. Haka kuma ba wanda ya taɓa nuna baƙin cikinsa ko ɓacin ransa a lokacin da shanunsa ko
tumakinsa da awakinsa ko talo-talo ko agwagi da kajin da yake kiwo suka samu
yawan albarkar ’ya’ya! Sannan kuma a iya saninmu da tarihin rayuwar al’ummomin
duniya, ba a taɓa
samun waɗansu
mahankalta da suka nuna ƙyamatar yawan haihuwar ’ya’ya a cikin jama’arsu
ba!
Sai a waɗannan ’yan shekarun na ƙarshen zamani ne da
gaskiyar imani da sakankancewar mutane da Allaah ta yi kaɗan, tawakkalinsu ga Mahaliccinsu Ubangijin
Halittu ya yi rauni, shi ne muke jin labarin yadda waɗansu shugabanni kamar na ƙasar
Sin sun gwada kafa wa mutanensu dokar hana haihuwa bayan ɗa na farko! Amma tun kafin a yi nisa sai
su da kansu suka fahimci mummunar ta’asa da ɓarnar da bin wannan dokar za ta jawo musu:
Na yawaitan tsofaffi da ƙarancin yara matasa, da kuma yawaitan maza da ƙarancin
mata a cikinsu! Don haka, nan da nan suka janye wannan shu’umar doka, suka zauna lafiya!
To, me ya sa mu kuma a yau muke ta ƙoƙarin
yin aiki da abin da waɗansu
suka gwada suka ga rashin alfanunsa? Alhali kuma ya ci karo da koyarwar sahihin
addininmu da kyawawan al’adunmu?!
[3] Mu musulmi mun riga mun yi imani cewa: Kowane ɗa arzikinsa a hannun Allaah Ta’aala ya ke,
kamar yadda ya nuna a cikin Suratul An’aam:
وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُمْ مِنْ إِمْلَاقٍ نَحْنُ نَرْزُقُكُمْ وَإِيَّاهُم
Kuma kar ku kashe ’ya’yanku saboda talaucin da
kuke ciki, mu muke azurta ku, da su kansu ’ya’yan.
Sannan kuma a cikin Suratul Israa’i, ya ce:
وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُمْ خَشْيَةَ إِمْلَاقٍ نَحْنُ نَرْزُقُهُمْ وَإِيَّاكُم
Kuma kar ku kashe ’ya’yanku don tsoron aukuwar
talauci, mu muke azurta su ’ya’yan, da ku kanku.
Waɗannan
ayoyi, in ji Malamai sun nuna haramcin kashe ’ya’ya saboda talaucin da iyaye
suke fama da shi a yanzu, ko kuma don tsoron aukuwar talaucin a nan gaba idan
suka ƙyale ’ya’yan a raye! Dayake a ayar farko iyayen
suna cikin talaucin ne sai ya fara lallashinsu da ambaton arzikinsu da farko
kafin na ’ya’yansu. Amma a aya ta biyu dayake ’ya’yan ne suke ji wa tsoron talaucin sai ya fara ambaton arzikin ’ya’yan kafin na iyayen!
A taƙaice dai, babu wata hujja ko wani dalili na ƙyamar
haihuwa ko ɗaukar
matakan daƙile cigaba da halittar abin da ke cikin ciki tun kafin bayyanarsa a duniya.
Allaahumma, sai dai in an tabbatar ko ana kyautata zaton aukuwar wata
matsananciyar wahala mai kaiwa, wataƙila ga salwantan rayuwar mai haihuwar ko
kuma abin da za a haifa, amma ba talauci ba! Domin a cikin Hadisin Sahabi
Abdullah Bn Mas’ud
wanda Al-Bukhaariy da Muslim suka fitar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya tabbatar mana da cewa, tun a lokacin da jaririn yake cikin cikin
mahaifiyarsa ne aka gama rubuta arziƙinsa:
ثُمَّ يَبْعَثُ اللَّهُ مَلَكًا فَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ وَيُقَالُ لَهُ اكْتُبْ عَمَلَهُ وَرِزْقَهُ وَأَجَلَهُ وَشَقِيٌّ أَوْ سَعَيدٌ
Sai kuma Allaah ya aika masa da Mala’ika, sai kuma
ya umurni da abubuwa huɗu, ya
ce da shi: Rubuta irin aikinsa, da arziƙinsa, da ajalinsa, da kuma ko ɗan Wuta ne ko kuma ɗan Aljannah.
Don haka, babu wani dalilin jin tsoron talauci ga
jaririn da aka haifa, ko wanda za a haifa a wurin duk wanda ya yi cikakken
imani da ƙudura da ikon Allaah Ubangijin Halittu Mabuwayi Mai Girma.
[4] Amma maganar wani cewa, a yau rayuwar ce ta yi
tsananin tsada sosai, ta yadda da wahala mutum yake iya ɗaukar nauyin karatun islamiyya da na bokon
’ya’yansa. Ga kuma kuɗaɗen abinci da magani da sutura da na sauran
buƙatun yau da kullum!
A gaskiya waɗannan duk abubuwa ne masu sauƙi, kuma ba komai ba ne
idan muka tuna abin da muka ambata a baya na yalwa da ƙarfi arziƙin da
ke wurin Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala . Amma rashin cikakken dogaro da rashin kyautatawa wurin neman halal
ne kawai matsalar. Don haka, maganin abin kawai shi ne: Duk mu samu cikakke
kuma kammalallen dogaro da biyayya ga Allaah, sannan mu tashi mu yi da gaske
kuma mu kyautata wurin neman halal don amfanin kanmu da zuriyarmu. A cikin
Hadisin da Ibn Maajah ya fitar da shi kuma As-Shaikh Al-Albaniy ya sahhaha shi
daga riwayar Umar Bn Al-Khattaab, Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya ce:
لَوْ أَنَّكُمْ تَوَكَّلْتُمْ عَلَى اللهِ حَقَّ تَوَكُّلِهِ ، لَرَزَقَكُمْ كَمَا يَرْزُقُ الطَّيْرَ ، تَغْدُو خِمَاصًا ، وَتَرُوحُ بِطَانًا
In da za ku dogara ga Allaah haƙiƙanin
dogaronsa, to da kuwa ya azurta ku irin yadda yake azurta tsuntsaye: Suna fita
da safe a cikin yunwa, kuma su komo da yamma cikin ƙoshi.
Idan har mun yarda yana da ikon warware wannan, ta
yaya sauran matsalolin za su gagare shi warwarewa, alhali shi ne Ubangijin
Halittu, Mai Rahama Mai Jin Ƙai?!
Daga bayan wannan sai kuma haɗin-kai da taimakon juna. Mu zama tsintsiya
ɗaya, kuma Hannun dama da
na hagu su riƙa cuccuɗawa suna wanke junansu cikin tausayi da ƙaunar
juna.
[5] Kowa ya yi haƙuri kuma ya yi ƙoƙarin ɗaukar nauyin abin da Allaah ya azurta shi
na ’ya’ya shi da kansa, kar ya ɗora wa
kowa daga cikin dangi da ’yan uwa da abokai ko malaman tsangaya wannan nauyin.
Kar kuma ya sake su sakaka suna ta gararamba a tituna da layuka, ba tare da
yana ilmantar da su, suna zuwa makaranta inda ake koya musu nagartaccen ilimi
da tsabta da sauran kyawawan ɗabi’u
da halaye ba.
Idan kuwa ya tabbatar ba zai iya ɗaukar nauyin iyalan da Allaah ya ba shi
ba, saboda tsufa ko rashin lafiya da tsananin ƙuncin rayuwa ko dai
sauran larurori makamantansu, to a nan ne ya halatta ya ɗauki matakan da suka dace kuma ba su yi
hannun-riga da koyarwar addini ba wurin bayar da tazarar haihuwar: Kamar ya
daina saduwar kwata-kwata a tsawon lokacin da mace take shayarwa, watau shekaru
biyu daidai ga wanda ke son kammala shayarwar, ko kuma ya riƙa yi
wa matar azalu da yardarta da amincewarta.
Domin ya tabbata a cikin hadisin Jaabir (Radiyal
Laahu Anhumaa) wanda Al-Imaam Muslim ya riwaito: Wani mutum ya taɓa zuwa wurin Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Ina da baiwa (kuyanga), ita ce mai yi mana hidima
kuma mai yi mana ban-ruwa a gonarmu, ni kuma ina kwanciya da ita, amma kuma ina
tsoron kar ta samu ciki? Sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya
ce:
اعْزِلْ عَنْهَا إِنْ شِئْتَ ، فَإِنَّهُ سَيَأْتِيهَا مَا قُدِّرَ لَهَا
Ka yi mata azalu in ka ga dama, amma fa abin da
aka ƙaddara mata zai zo mata.
Abin nufi da azalu shi ne: Ya zubar da maniyyinsa
a waje maimakon a cikin mahaifarta.
Amma fa wannan ba ya hana aukuwar duk irin abin da
Allaah Ta’aala ya ƙaddara halitta shi ga wannan matar.
(Domin ai mun sha jin labarin waɗanda suke ɗaukar matakan bayar da tazarar haihuwar ta
bin sababbin hanyoyin da ilimin likitancin zamani ya kawo sau-da-ƙafa,
amma daga ƙarshe sai kuma a gwammace da ma ba a ɗauki matakan ba! E, mana! To mace ce ta dakatar da
haihuwa na tsawon shekaru biyar, amma lokacin da ta zo haihuwar farko bayan ta
gama yin tazarar sai Allaah da ikonsa ya ba ta ’yan uku!!)
Yin watsi da waɗannan hanyoyin da ba su da wata matsala,
da komawa ga ɗaukar
matakan da ba irin wannan ba, kamar na cushe-cushen wasu robobi a cikin
mahaifa, ko na zarƙama wa mata allurai, ko ɗura musu ƙwayoyi iri-iri, waɗanda su kansu ƙwararrun likitoci sun
tabbatar cewa suna janyo waɗansu
matsaloli masu hatsari ga lafiyar mace da rayuwarta, bai dace ba. Saboda
Hadisin Ubaadah Bn As-Saamit da Ibn Abbaas wanda Ibn Maajah ya riwaito cewa,
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
لاَ ضَرَرَ وَلاَ ضِرَار
Babu fara cuta kuma babu rama cuta
Ma’ana: Bai halatta ba, kuma ma haram ne a fili ƙarara,
musulmi ya fara buɗe ƙofar
cutarwa ga ɗan’uwansa
musulmi, ko kuma musulmi su riƙa cutar junansu. Allaah ya kiyaye, Allaah ya tsare
mu.
[6] Su kansu ƙungiyoyin da suka yarda
da bin wannan hanyar ta dakatarwa ko ƙayyadewa ko bayar da tazarar haihuwa a
cikin jama’a sun
sanya mata ƙa’ida ko sharaɗin
cewa: Sai an samu amincewar ma’aurata. Watau, sai bakin ma’aurata ya zo ɗaya a kan amincewa da bin wannan hanyar.
Amma a samu wasu mazaje, kamar yadda ya zo a cikin wannan tambayar, suna fitina
da tilasta wa matan aurensu kan haka, tare da yi musu barazanar hana su haƙƙoƙinsu
na kyautata zamantakewa, kamar ta hana su abinci da tufafi da magani da
sakin-fuska da rabon-kwana da sauransu, wannan kam cuta ce kuma zalunci ne a
fili ƙarara, wanda kuma Allaah Maɗaukaki
zai yi sakayya a kansa wataƙila ma tun daga nan duniya kafin zuwa Lahira!
A cikin Al-Musnad, Ahmad ya riwaito Hadisin da
Shu’aib Al-Arnaa’uut (Rahimahul Laah) ya sahhaha shi saboda yawan hanyoyinsa,
daga Abu-Hurairah daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
وَدَعْوَةُ الْمَظْلُومِ تُحْمَلُ عَلَى الْغَمَامِ ، وَتُفْتَحُ لَهَا أَبْوَابُ السَّمَاءِ ، وَيَقُولُ الرَّبُّ عَزَّ وَجَلَّ : وَعِزَّتِي لَأَنْصُرَنَّكَ وَلَوْ بَعْدَ حِينٍ
Kuma addu’ar wanda aka zalunce shi ana ɗaukarta a kan giragizai, kuma ana buɗe mata ƙofofin sama, kuma
Ubangiji Mabuwayi Mai Girma yana cewa: Na rantse da Buwayata, lallai zan
taimake ka, ko da nan gaba ne!
Sannan wani abin da yawancin mutanenmu ba su cika
mayar da hankali gare shi ba game da wannan matsalar shi ne: Me ya sa ba a damu
da yaɗa
wannan kiraye-kirayen a cikin maƙiyanmu da abokan hamayyanmu ba? Me ya sa ba ma jin
hakan a cikin abokan zamanmu da cikin maƙwabtanmu na kusa ko na-nesa? Me ya sa muke
jin a wasu wuraren da ƙasashe ma har kyauta ake bayarwa ga iyalan da suka
haihu? Don me su suke ƙoƙarin yawaita jama’arsu mu kuma muna ƙoƙarin rage namu?!
Wataƙila wani ya ce, ai tattalin arziƙinmu
ne bai yi ƙarfi irin na su ba!
Haba jama’a! Wane irin arziƙi ne a duniya Allaah bai
yi mana ba? Ko kuwa dai kuna nufin: Yawan mahandama da masu baba-kere da masu
ruf-da-ciki da almubazzarai da maɓarnata
da marasa tunani da hangen nesa, kuma marasa kishin ƙasa da kishin jama’arta ne da ba su da shi, waɗanda mu kuma suka yi mana katutu?! In ba
haka ba, ai tuni Allaah Ta’aala ya ce:
وَمَا مِنْ دَابَّةٍ فِي الْأَرْضِ إِلَّا عَلَى اللَّهِ رِزْقُهَا
Kuma babu wata dabba a doron ƙasa face arziƙinta
yana hanun Allaah ne.
Sannan ita kanta haihuwar ma ba arziƙi ba
ce?!
(Akwai gidajen da Allaah ya ba su arzikin ’ya’ya
kuma aka yi shaidar cewa talauci ya yi musu katutu, amma daga baya sai ga shi
Allaah Mayalwacin Sarki ya azurta su har labarinsu ya yaɗu a ko’ina cewa sun koma gidaje na
mawadata!)
Sannan kuma ban da wannan, saboda sakaci da halin
ko-oho da muke da shi, a yau akwai hanyoyi da yawa da ake bi domin illata mu da
daƙile yawanmu da ƙara raunana mu, kamar ta: Yaɗa muggan makamai a cikin matasanmu, da
yawaita shaye-shayen ƙwayoyi da kayan maye masu daskarar da ƙwaƙwalwa
a cikinsu, da ƙirƙiran yaƙe-yaƙen babu-gaira babu-dalili a cikin jama’armu, ga kuma gurɓata kayan abinci da ruwan sha, da lalata
tsire-tsire da zurriya, da kiraye-kirayen hana auren-wuri da ƙayyade
shekarun aure a tsakanin samari da ’yan mata, da halatta zubar da ciki, da shan
magungunan hana ɗaukar
cikin, da yi wa yara allurorin da suke cutar da jiki da sunan rigakafi da
sauransu. To, don me za mu taimaka wa maƙiyanmu har su samu ikon cin nasara a
kanmu?!
[7] A ƙarshe, kar wani miji ya yi tunanin cewa
rashin amincewar matarsa ga ɗaukar
wani matakin ragewa ko ƙayyadewa ko dakatar da haihuwa wai wannan ya ba
shi damar ya danne mata haƙƙoƙinta, ko na abin da ta haifa ko abin da za ta
haifa a shimfiɗarsa,
kar ya yi tsammani wannan ya isa ya hana shi yi mata adalci a tsakaninta da
sauran kishiyoyinta, ko kuma ya ɗauka
hakan ba zunubi ko saɓo ba
ne! Al-Imaam Abu-Daawud da Ibn Maajah sun riwaito Hadisin da Al-Imaam
Al-Albaaniy ya sahhaha shi daga riwayar Abu-Hurairah cewa Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
مَنْ كَانَتْ لَهُ امْرَأَتَانِ فَمَالَ إِلَى إِحْدَاهُمَا جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَشِقُّهُ مَائِلٌ
Duk wanda yake da matan aure guda biyu sai ya
karkata zuwa ga ɗayarsu,
to zai zo a Ranar Ƙiyama da sashen jikinsa a shanye!
Sanannen abu ne cewa: Abin da ake nufi da karkata
a nan ita ce: Dukkan karkata na fili ƙarara, ba ƙaramar karkata ta zuci
ba wadda har Annabawa ma ba su da iko a kanta. Kuma wannan ita ce irin karkatar
da Allaah ya hana, ya ce:
فَلَا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوهَا كَالْمُعَلَّقَة
Kar ku karkata dukkan karkata, har ku bar ta kamar
wata ratayayya
Wannan kaɗai ya isa wa’azi da gargaɗi ga dukkan mai imani a musulunci, in shã
Allãh .
Allaah ya ƙara mana tabbata da kafewa a kan bin Alƙur’ani da Sunnah Sahihiya kamar yadda
magabatanmu na ƙwarai suka fahimta.
WALLAHU A'ALAM
Wa Sallal
Laahu Alaa Nabiyyinaa Wa Aalihi Wa Sahbihi._
Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.