Ticker

6/recent/ticker-posts

Hashimu Uban Maza

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Hashimu Uban Maza

Hashimu Uban maza ɗan garin Tcibiri ne ta yankin Maradun ta jihara Zamfara. Yana da ƙaƙarin aikin gona don haka Amali ya yi masa waƙa.

 

    G/Waƙa : In zo mu ga hashimu uban maza,

: Namijin ƙwazo ba shi gasuwa.

 

Jagora: Hashimu guda ne muka gani,

‘Y/Amshi: In za ku hwaɗa mana ina wani?

: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.

 

Jagora: Gyado tahi duƙe ga gaban ƙasa.

‘Y/Amshi: Mu gane ka idonka na masassari[1],  

: Namijin ƙwazo baka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.x2

 

Jagora: Shi dai gona ba ta ɗauke noma nai,

  : Sai dai karkara isa noma,

  : Ko ‘Yah Hali ba ta nan,

  : Balle kuma ‘Yah Hali na kusa,

  : In ya nome ita ka hizge hannunai,

  : Ta yo gida da shi,

  : To in bata tarbe ba ba shi dawowa birni,

  : Mi yakai gida?

  ‘Y/Amshi: Sai dai ya shige dawa kamad damo.

: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.

 

 Jagora: Gyado[2] tahi gicce ga gaban ƙasa.

  ‘Y/Amshi: Mu gane ka idonka na masassari[3],

: Namijin ƙwazo baka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.

 

 Jagora: Sabon gero mai tagomashi Ɗanmantu,

  : Abin zaman gari,

  : Danginka suna kwaɗan zama da kai,

  : Dattiɓe suna kwaɗan zama da kai,

  : ‘Yan yara suna kwaɗan zama da kai,

  : Matanka suna kwaɗan zama da kai,

  : Mai son ka yana kwaɗan zama da kai,

  : Yau kowac ce ba ya son ka ya saɓa,

  : Ba shi ne da ranka ba.

   ‘Y/Amshi: Balle ya hana maka ka kwan biyu.

: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.

  Jagora: Ko can giwa ita ka haihuwag giwa,

: Kowa na ganin kama,

: Ita dai kura ba mu san bunsurunta ba,

   ‘Y/Amshi: Sai dai ta hi huskata[4] karen ɓuki,

: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.

 

  Jagora: Shi ya aika in taho garai,

: Ban samu zuwa ba,

: Sai da anka kwana biyu,

: Yac ce ban gane ka ba,

: Ni ko nic ce gani nan tahe,

: Niɗ ɗauki duma ni azo ma barwaina,

: Dan nan nis shigo gaba,

: Han nij ji ana gardama gari,

: Wasu na cewa ga Amali can,

: Wasu ko sun ce ba Amali ne ba,

: A a abin can Amali ne yad danno,

: Koje uban ɗumi,

: Waɗanga da nac ce Amali ne sun kayat,

: Su nay yi hankali,

: Dan nan daɗa nig gangaro gari,

; Yab ba mu hura sai da munka bat ta gari,

: Yac ce bat ta nan ku sha,

: Yab ba mu tuwo sai da munka bas shi gari,

: Yac ce bas shi nan ku ci,

: Sannan ga goronmu ya isa,

: Sannan ga tabammu ta isa,

: Sannan kuma yab ba ni tagguwa[5],

: Ka san kau taggon ga ya hi riga,

: Ko an ɗunke shi tagguwa,

: Wata ‘yar riga ba ta kai garai,

: Yab ban naira arba’in da shidda mu ɗauka,

: Mu sai ruwa mu sha,

‘Y/Amshi: Yac ce a haɗa muna mu tai gida.

: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.

 

Jagora: Kowa aika nit taho garai,

: Ko ya ba ni kaɗanna,

: Ba ni rena girma nai,

: Sai dai in yi mai kaɗan,

: Marai nike mai kirmtcin ɗumi Ɗan Isah,

: Koje uban batu,

: Suda nike mai sintirin ɗumi ta-ta-ta,

: Had dai ta hihhika.

‘Y/Amshi: Daɗin maganammu da ƙaraurawa,

: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.x2

 

Jagora: Dab bakin yaƙi ana ganin yunwa,

: Amma ba a ga tcada ba,

: Dag kakanninmu har uwayenmu,

: Kowa bai ga tcada ba,

: Bakin tsaba duk tiya ta kai sitta,

: Dan nan ai ta hanƙuri,

: Dan nan kuma har anka sa tarau[6],

: Dan nan tak Koma sule biyu,

: Dan nan kuma har anka sa tarau,

: Yanzu tiya ba ta taɓuwa,

: Kaman naira shidda za ka cin kwano,

: Amma ba na cin dare,

: Duniyar ba mu gane ma kanta ba,

: Wasu na tashi suna barin ƙasa,

: Wasu na Komowa zuwa gida,

: Wasu kau sun dai ɗauki hanƙuri,

: Duniya ba a gane ma kanta ba,

: Allah ya bamma kainai sani,

; Kowa na aikin rashin gani.

‘Y/Amshi: Allah ka aza mu ga abin ƙwarai.

: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.

 

Jagora: Hashimu guda ne na Tcibiri[7],

: Hashimu guda ne munka gani.

‘Y/Amshi: In zaku hwaɗa mana ina wani?

: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.

 

     Jagora: Bana an yi hwari[8] munka sha wuyar noma,

: Kwana arba’in da ɗai ba sanyi,

: Muna ganin wuya,

: Ga gero duk kunnuwashi sun bushe,

: Kowa na ta zullumi.

‘Y/Amshi: Namijin ƙwazo ba ka gasuwa[9],

: In zo mu ga Hashimu Uban maza.



[1]  Idanu suna kamar su rufe saboda wahala.

[2]  Wata dabba ce mai haƙora zago-zago, yana amfani da haƙoransa ne wajen tonon ƙasa.

[3]  Ƙifce-ƙifcen ido.

[4]  Fuskantar, ta fi yin kama da wani abu.

[5]  Yadin da zai ɗunka sutura.

[6]  Kwabo da ɗari.

[7]  Sunan wani gari ne a jamhuriyar Nijer.

[8]  Yankewar ruwan sama a lokacin damina, wanda kan sa yabanya ta fara bushewa don rashin ruwa.

[9]  Ba a iya gasarsa wajen aiki.

Post a Comment

0 Comments