Ticker

6/recent/ticker-posts

Ada Masu Wa Aiki Takakka

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ada Masu Wa Aiki Takakka

Ada masu wa aiki takakka a garin Kuka Tara yake a gundumar Katuru ta ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara. Ya shahara wajen aikin noma, don haka ya sami waƙar Amali.

 

G/Waƙa : Sai na zo in ga Ɗan Mamman in gaisai,

:  Za ni ga Ada masu wa aiki takakka.

 

  Jagora: Ada ya daure ma Jatau bai korai ba,

 : Ada ko can ba ya kyamam mai roƙo nai.

    ‘Y/Amshi: Ada ko can ba ya ƙyamam mai roƙo nai.

: Sai na zo in ga Ɗan Mamman in gaisai, :  Za ni ga Ada masu wa aiki takakka.

 

   Jagora: Ada nau Ɗan Alhajin Allah mai gero.

    ‘Y/Amshi: Ba ni buhun dawa,

: Mu bay yawon ganoma[1]

 

   Jagora: Ada nau Ɗan alhajin Allah mai gero,

    ‘Y/Amshi: Ada ya tcere ma mai yawon ganoma.

 

   Jagora: Ada nau Ɗan alhajin Allah mai gero.

 : Ba ni buhun dawa ka ban doki taka-hau[2],

    ‘Y/Amshi: Ba ni buhun dawa ka ban doki taka-hau,

 : Sai na zo in ga Ɗan Mamman in gaisai,

: Za ni ga Ada masu wa aiki takakka.x2

 

 Jagora: Sai na zo in ga Ɗan Mamman in gaisai,   : Za ni ga Ada masu wa aiki takakka.

   ‘Y/Amshi: Sai na zo in ga Ɗan Mamman in gaisai,  : Za ni ga Ada masu wa aiki takakka.

 

  Jagora: Za ni ga Ada na ji labarin huɗatai,

 : Ni ishe shani nai cikin daji na noma,

 : Shi ko ya hunce yana ɗamrin walkinai,

 : Duw wada kas san guguwad daji na sauri,x2

   ‘Y/Amshi: To haka nan yaw wa hakin daji baki ɗai.

 : Sai na zo in ga Ɗan Mamman in gaisai,

: Za ni ga Ada masu wa aiki takakka.x2

 

     Jagora: Ada ya daure ma Jatau bai korai ba,

 : Ada ko can baya kyamam mai roƙo nai,

‘Y/Amshi: Ada ko can baya ƙyamam mai roƙo nai.

 

     Jagora: Ada nau Ɗan alhajin Allah mai gero.

‘Y/Amshi: Ada ya tcere[3] ma mai yawon ganoma.

 : Sai na zo in ga Ɗan Mamman in gaisai,

: Za ni ga Ada masu wa aiki takakka.



[1]  Neman aikin gona kamar noma a gonar wani don ya biya.

[2]  Dokin da aka haɗa shi da sirdi aka bayar, wato iyakar wanda aka bai wa dokin hawa.

[3]  Wucewa.

Post a Comment

0 Comments