Gwauro (Dudu)

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Gwauro (Dudu)

    Amadu ne sunansa a garin Gidan Nababba yake na  Æ™asar Shinkafi ta jihar Zamfara. Amali ya yi masa waÆ™a ne saboda zamansa gwauro na tsawon lokaci.

     

       G/WaÆ™a : Sannu da gaskanta[1] wuta,

    : Sannu da gaskanta wutas sanwa,

     

     Jagora: Sannu da gaskanta wuta.

    ‘Y/Amshi: Sannu da gaskanta wuta,

    : Sannu da gaskanta wutar sanwa,

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci,

     

     Jagora: Sannu da gaskanta wuta dai,

    ‘Y/Amshi: Sannu da gaskanta wutar sanwa,

    : Mi za ta yi ma?  

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Sannu da gaskanta wuta gwauro,

    ‘Y/Amshi: Sannu da gaskanta wutar sanwa.

     

     Jagora: Na É—oke ka lambuwal[2],

    : Sabon injin na ƙasar isa,

    ‘Y/Amshi: Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Na É—auke ka lambuwal.

    ‘Y/Amshi: Sabon injin na Æ™asar Isa.

     

     Jagora: Komai lokaci garai.

    ‘Y/Amshi: Don haka yac ce,

    : Mu yi mai waƙa.

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci,

     

     Jagora: Komai lokaci garai.

    ‘Y/Amshi: Don haka yac ce,

    : Mu yi mai waƙa,

     

     Jagora: Gaggarje bushi[3] wuta.

    ‘Y/Amshi: Yanzu ta kama,

    : Mu ga haskenta.

     

     Jagora: Gaggarje bushi wuta,

    ‘Y/Amshi: Yanzu ta kama,

    : Mu ga haskenta,

     

     Jagora: Sa mata hwanho[4],

    : Mu ga haskenta,

    ‘Y/Amshi: Yanzu ta kama,

    : Mu ga haskenta,

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Dudu tun yana da mata tai,

    : Ya ima daka,

    : Ya iya wankin surhe.

      ‘Y/Amshi: Ya iya cincimta ruwan sanwa.

    : Mi za ta yi ma?

     : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Dudu tun yana da mata tai,

    : Ya ima daka ,

    : Ya iya warkin Surhe,

    ‘Y/Amshi: Ya iya cimcimta ruwan sanwa.

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro barka da walaƙanci,

     

     Jagora: An aike shi kassuwa,

    ; Ya ishe rogon taɓe,

    : Dudu yab bada taro,

    ‘Y/Amshi: Yak kaÉ“e saye,

    : Da hushin hwarin.

    : Mi zata yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Gaggarje bushi wuta,

    ‘Y/Amshi: Yanzu ta kama,

    : Mu ga haskenta.

     

     Jagora: Dudu ka Æ™i yin tsawo.

    ‘Y/Amshi: Don kada tsaba,

    : Ta ga damak ka.

    : Mi zata yima?

    : Gwauro barka,

    : Da walaƙanci.

     

     Jagora: Amadu ka Æ™i yin tsawo.

    ‘Y/Amshi: Don kada reda[5],

    : Ya ga damak ka.

    : Mi zata yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Ka san in ana kiÉ—in bindiga,

    : Ba a jin amon ƙyestu,

    : In kana daka,

    : Dudu mata su aje,

    ‘Y/Amshi: Sai ka kirÉ“a a ji É—an nasu,

    : Mi za ta yima?

    : Gwauro barka,

    : Da walaƙanci.

     

     Jagora: Sai ka kirÉ“a su hito su kau.

    ‘Y/Amshi: Sai ka kirÉ“a aji É—an nasu.

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro barka,

    : Da walaƙanci.

     

     Jagora: Ga Dudu yana daka,

    : Ga mata suna daka,

    : Amma ba a jin dakan mata,

    : Nashi ya haye.

    ‘Y/Amshi: Mun ishe ya sa,

    : RibiÉ—in hwarin.

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Ga Dudu yana daka,

    : Ga mata suna daka,

    : Amma ba a jin dakan mata,

    : Nashi ya haye.

    ‘Y/Amshi: Mun ishe ya sa,

    : RibiÉ—in[6] hwarin.

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Gwauro,

    : In ana tsaron tsuntsu,

    : Ba ya cin tuwo,

    : Kuma dai ba ya shan hura,

    : Yayin cin tumu[7] yakai.

    ‘Y/Amshi: Can yaka lalata hatci daji,

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Amadu in ana tsaron tsuntsu,

    : Ba ya cin tuwo,

    : Kuma dai ba ya Shan hura,

    : Yayin cin tumu yakai.

    ‘Y/Amshi: Can yaka muzanta hatci daji.

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Duk gonar da kak karam ma tumu[8],

    : Ta É“ace É“ari,

    : Wannan ba ta yin da,

    ‘Y/Amshi: In ka ga hatci tsaitsaye bici[9] ne,

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci,

     

     Jagora: Babu hatci tsaitsaye ya zwage,

    ‘Y/Amshi: In ka ga hatci tsaitsaye bici ne,

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro,

    : Barka da walaƙanci.

     

     Jagora: Gaggarje[10] bushi wuta.

    ‘Y/Amshi: Yanzu ta kama muga haskenta,

     

     Jagora: Sannu da kamkamta wuta,

    ‘Y/Amshi: Sannu da kamkamta wuta,

     

     Jagora: Dole ka kamkamta wuta Amadu,

    ‘Y/Amshi: Dole ka kamkamta wutas sanwa,

     

     Jagora: Amadu barka da walaÆ™anci,

    ‘Y/Amshi: Amadu barka da walaÆ™anci,

     

     Jagora: Gwauro barka da ganin reni.

    ‘Y/Amshi: Gwauro barka da walaÆ™anci.

     

     Jagora: Amadu barka da zama ‘yamti[11],

    ‘Y/Amshi: Amadu barka da zama ‘yamti.

    : Mi za ta yi ma?

    : Gwauro barka da walaƙanci.

     

    4.0.5 Gwauro (Ma’azu)

    Ma’azu wani Bafulatanin daji ne Amali ya yi wa wannan waÆ™a. A garin  Sububu yake ta Æ™aramar hukumar Maradun a jihar Zamfara. 

     

       G/WaÆ™a : Sai na taho ga mai huskar shanu,

    : Mai kamar kare ya katce.

     

     Jagora: Sai na taho ga mai huskar shanu.

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskar shanu,

      : Ga Ma’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Sai na taho da mai hikimar banza,

      : Mai kamar kare ya gibce.

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskar shanu,

      : Ga Ma’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Gwauro mai hankalin sayaki[12].

    ‘Y/Amshi: Gwauro mai hankalin katsattcen doki,

      : Sai na taho ga mai huskas shanu,

      : Ga Ma’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Gwauro mai hankalin sayaki.

    ‘Y/Amshi: Gwauro mai hankalin katsattcen doki,

      : Sai na taho ga mai huskas shanu,

    : Ga Ma’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Ba bin gari ya kai ba.

    ‘Y/Amshi: Sai ya bi shalla ya É—ora kukan mesa,

    : Sai na taho ga mai huskar shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Ba bin gari shi kai ba.

    ‘Y/Amshi: Sai ya bi shalla ya É—ora kukan mesa.

     

     Jagora: Ƙannenka sun hana maka twatsa,

      : Sun bakka nan ga kwamtsad ebe[13],

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga huskar shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Ƙannenka sun hana ma twatsa.

    ‘Y/Amshi: Sun bakka nan ga kwamtsad ebe,

      : Sai na taho ga huskar shanu ,

    : Ga Mu’azu gwauron daji,

     

     Jagora: Kai ku ji banza ta gane banza,

    ‘Y/Amshi: Mu’azu gwauro da kudaku[14] nai daji.

     

     Jagora: Banza ta shikka banza,

    ‘Y/Amshi: Mu’azu gwauro da kudaku nai daji,

     

     Jagora: Kai ku ji noma ta no,.. kai!

    ‘Y/Amshi: Mu’azu gwauro da kudaku nai daji,

     

     Jagora: Kai ku ji banza ta noma banza.

     

    ‘Y/Amshi: mu’azu gwauro da kudaku ya noma,

      : Sai na taho ga huskad banza ga,

      : Mu’azu gwauron daji,

     

     Jagora: Gwauro mai hankalin sayaki,

    ‘Y/Amshi: Gwauro mai hankalin katcattcen doki,

     

     Jagora: Taho mai kama da É—an kai hwata,

    ‘Y/Amshi: Taho mai kama da turmin kuka,

     

     Jagora: Taho mai kama da bangon zaure,

    ‘Y/Amshi: Taho mai kama da turmin kuka.

      :Sai na taho ga mai huskad shanu,

      : Ga ma’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Gwauro bai san halin batun mata ba,

      : Sai ga mu’azu ya kai sisi.

    ‘Y/Amshi: Sai nataho a mai huskad shanu ga,

      : Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: ‘Yan nan tac ce ina jiranka dan nan,

      : Sai ga Mu’azu ya kai sittah[15],

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskad shanu,

      : Ga mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Rannan yas saida zakarunai,

      : Dan nan sai ga Mu’azu ya kai ukku,

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Rannan yas saida akuyatai dannan,

      : Sai ga mu’azu ya kai nera.

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskad shanu, 

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

        

     Jagora: Rannan yas saida tunkiyatai dan nan,

      : Sai ga Mu’azu ya kai fefa.

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga huskas shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora  : Tac ce Mu’azu ya kai kuÉ—É—i,

      : Bai zo wurin batun hira ba.

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji,

     

     Jagora: An ce Mu’azu ya kai kuÉ—É—i, 

      : Bai zo wurin biÉ—ad aure ba.

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     Jagora  : Shi ko rannan Mu’azu sai yag gyara,

      : Rannan Mu’azu sai ya uhwa[16],

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskad shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Yac ce ‘yan Tubali salamu alaikum,

    ‘Y/Amshi: Yau na taho biÉ—ad kunkunne[17],

      : Sai na taho ga mai husakas shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Sai na taho ga mai hikimab banza,

    : Mai kamak kare ya girtce.

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Banza ta gane banza ga Mu’azu,

      : Gwauro da kudaku nai daji.

    ‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

      : Ga Mu’azu gwauron daji.

     

     Jagora: Banza ta gane banza. 

     ‘Y/Amshi: Ga Mu’azu gwauro da kudaku nai Daji.



    [1]  Shirya itace ko wani makamashi don kunna wutar sanwa.

    [2]  Na farko/lamba ta É—aya.

    [3]  Hura wuta da iskan baki.

    [4]  Busa iska.

    [5]  NiÆ™a

    [6]  Dakan gero har ya yi gari bayan an surfe.

    [7]  Zangarniyar gero wanda akan zaÉ“a a gasa a kware a ci.

    [8]  Gero wanda ya fara Æ™usa mai ido, wanda manoma kan É—ebo su kawo gida a riÆ™a gasawa anai murmutsawa ana ci

    [9]  Gero wanda bai yi ido ba marar Æ™wari.

    [10]  Dagewa.

    [11]  Zama babu mata.

    [12]  Kura.

    [13]  ‘Yayan nunu da ake fasawa a cinye tuwon, wannan tuwon da ke ciki shi ake kira ebe.

    [14]  Dankali.

    [15]  Sule da sisi.

    [16]  Tserewa/Guduwa

    [17]  Mata don a aura.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.