Ticker

6/recent/ticker-posts

Gora Uwat Tuwo

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Gora Uwat Tuwo

Gora mutumiyar Gidan bisa ce ta cikin ƙaramar hukumar mulkin Maradun, amma tana aure a garin Gidan Nababba a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Shinkafi, duk a cikin jihar Zamfara. A can take tuwo-tuwo, kuma ta shahara ga sana’ar don haka Amali ya yi mata waƙa.

 

    G/Waƙa : Za ni ga Gora uwat tuwo,

: Ta  Sa’idu buƙatakki ta biya,

    

    Jagora: Ni dai wance miyakki,

: Ban ga ta yi ba,

     ‘Y/Amshi: Tun ban lasa ba,

: Ga ƙuda ciki,

: Za ni ga Gora uwat tuwo,

: Ta  Sa’idu buƙatakki ta biya,

 

    Jagora: Ai na ga tuwonki wance,

: Sai makaho,

: Sai ko wanda ba gida kusa,

: Da ya ci tuwon kwabo,

: Ya burkuce hanji,

    ‘Y/Amshi: Sai zuwa wurin amai,

: Za ni ga Gora uwat tuwo,

: Ta  Sa’idu buƙatakki ta biya,

 

   Jagora: Mu dai ga Gora mun kawo hari[1],

: In na ishe Gora tana gida,

: Kurawa sai in yi hira nan,

: In na ishe Gora ba ta gida,

: Ɗan Goje in wuce,

: Ta Maguru,

    ‘Y/Amshi: Za ni ga Gora uwat tuwo,

: Ta  Sa’idu buƙatakki ta biya,

 

    Jagora: Ga Ummaru ya yanka saniya ta kwabe[2],

: Ta yi mai ƙwarai-ƙwarai,

: Ga Gora ta taho da kwano,

: Ta ce Sanda ga ni na taho,

: Ta sai ƙassan[3] goma sha bakwai,

: Ta sai tsoka ta hwan huɗu Kuma,

: Ga tosshi[4] ta sawo da yaji,

: Ga kinba da ciitta ta sawo,

: Gyara miyakki mai halin ɗiya,

: Da ka ci tuwonta sai zuhwa ya kubcikke ma,

: Sai ka yi santi.

    ‘Y/Amshi: Sannan ka ji jiɓi yana yima ƙawa[5],

: Za ni ga Gora uwat tuwo,

: Ta  Sa’idu buƙatakki ta biya,

 

     Jagora: Allah ya baki martabar miya, x2

‘Y/Amshi: Kuma Allah yai miki hwarin jini,

: Za ni ga gora uwat tuwo,

: Ta Sa’idu buƙatakki ta biya.

 

    Jagora: Kuma Allah yai maki hwarin jini,

    ‘Y/Amshi: Kuma Allah yai miki hwarin jini,

: Za ni ga gora uwat tuwo,

: Ta Sa’idu buƙatakki ta biya.

 

   Jagora: Ni dai wance miyakki,

: Ban ga ta yi ba,

    ‘Y/Amshi: Tun ban lasa ba,

: Ga ƙuda ciki,

: Za ni ga Gora uwat tuwo,

: Ta  Sa’idu buƙatakki ta biya,



[1]  Kai ziyara.

[2]  Ta yi kitse.

[3]  Ƙashin miya

[4]  Barkono

[5]  Zufa ga fuska

Post a Comment

0 Comments