Ticker

6/recent/ticker-posts

Magajin Gera

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Magajin Gera

Wannan waƙar sarauta ce wadda Amali ya yi wa magajin garin Gera. Shi ke riƙon garin don haka Amali ya yi masa waƙar don ya ƙara masa kwarjini ga jama’arsa.

 

G/Waƙa : Na zo garkar[1] Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka arzikin,

: Shirya mutanen yau.

 

   Jagora: Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka arzikin,

: Shirya mutanen yau.

   ‘Y/Amshi: Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka hankalin,

: Shi ka riƙon Gera.

 

   Jagora: Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka arzikin,

: Shirya mutanen yau.

    ‘Y/Amshi: Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka hankali,

: Kai ka riƙon Gera.

 

  Jagora: Magaji harshe zauna,

: Cikin haƙori ka yi wadagi[2],

: Ana son a taɓa ka Jallah,

: Bai bada umurni ba.

   ‘Y/Amshi: Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka arzikin,

: Shirya mutanen yau.

 

   Jagora: Karen ɓuki da biri,

: Ku dakata dai ku ji ɓannakku,

: Inda duk ba ka ƙosa ba,

: Ba ka fatar ka yi jayayya.

   ‘Y/Amshi: Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka arzikin,

: Shirya mutanen yau.

 

   Jagora: Inda duk ba ka ƙosa ba,

   ‘Y/Amshi: Ba ka fatar ka yi jayayya,

 

   Jagora: Sai godiya Makau gaida Bawa,

   ‘Y/Amshi: Ya yo mana alheri[3]. X2

 

   Jagora: Ubandawakin noma.

   ‘Y/Amshi: Mu gaida shi yai mana alheri.

 

   Jagora: Mu gaida zakin noma na Gera,

   ‘Y/Amshi: Ya yo mana alheri. X 2

  : Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka arzikin,

: Shirya mutanen yau.

 

   Jagora: Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka arzikin,

: Shirya mutanen yau.

    ‘Y/Amshi: Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

: Allah ya ba ka arzikin,

: Shirya mutanen yau.



[1]  Ƙofar gida.

[2]  Gadara/walwala.

[3]  Kyauta

Post a Comment

0 Comments