Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yak Kolo

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

‘Yak Kolo

Mutumiyar Batamna ce ta ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, Ita ma ‘Yak Kolo ta samu fice ne ga sana’ar tuwo-tuwo a garin Batamna, duk mai cin tuwu a Batamna ya san ‘Yakkolo mai tuwo domin shahararr da ta yi, hakan ya sa Amali ya ziyarce ta har ya waƙe ta.

 

 G/Waƙa : Ta ɗauki yau da gobe,

: Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

  

     Jagora: ‘Yak Kolo ke iya tuwo,

‘Y/Amshi: ‘Yak Kolo ta iya dakan gero,

: Ta ɗauki yau da gobe,

: Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

     Jagora: Ɗiyar Arju nit taho gani. X2

‘Y/Amshi: Yau gani ga Dela da ni da yarana. X2

: Ta ɗauki yau da gobe,

: Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

     Jagora: Kullun nama taka saye,

: Ta aza shi ga murhu ya sha wuta,

: Kuma ga twasshi ta haɗa da yaji,

: Ga kalwa[1] ta haɗa tana ƙamshi.

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

     Jagora: Kullun nama taka saye,

: Ta aza shi ga murhu ya sha wuta.

: Kuma ga twasshi ta haɗa da yaji,

: Ga kalwa ta haɗa da man shanu.

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

     Jagora: Ɗiyar Arju nit taho gani. X2

‘Y/Amshi: Yau ga ni ga Dela da ni da yarana. X2

: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

     Jagora: Kullun nama taka saye,

: Ta aza shi ga murhu ya sha wuta,

: Ga twasshi ta haɗa da yaji,

: Ga kalwa ta haɗa tana ƙamshi.

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

     Jagora: In na kai gaisuwa ga Dela,

: Sai ta sa man tuwo na sitta[2],

: Naman sitta ta lema man shanu,

: Kuma sannan ta bani fefa.

‘Y/Amshi: In ansa in saka ga aljihu,

: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

Jagora: Tuwon Rakkiya tuwo ne,

: Wannan na ci shi lahiya nik kwan.

‘Y/Amshi: Wannan na ci shi lahiya nik kwan.

 

Jagora: Tuwo ba a kai ga Dela,

‘Y/Amshi: Sai kau Gora da A’i Sattete[3]. X2

 

     Jagora: Tuwon Rakkiya tuwo ne,

: Wannan na ci shi lahiya nik kwan,

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo,

 

Jagora: Gora ta biyani doki[4],

: Ba ƙarya ce ba nih hwaɗi tai man.

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

Jagora: Da na ci tuwon wance nai kasala,

: Ran nan na kwana ɓamɓaraƙ ƙyaure.

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

Jagora: Na ci tuwon wance na yi raki.

‘Y/Amshi: Ran nan ya kwana ɓamɓaraƙ ƙyaure,

: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

     Jagora: Kaɗan nika nawa ga tashi,

: Sai ka ga bayan gari ga wandona,

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

Jagora: A’in K.K ta yi doki,

: Ba ƙarya ce ba nih hwaɗi ta yi.

‘Y/Amshi: Ba ƙarya ce ba kah hwaɗi ta yi.

Jagora: Gora ta biya ni nata,

: Ba ƙarya ce ba nih hwaɗi ta yi.

‘Y/Amshi: Ba ƙarya ce ba kah hwaɗi ta yi,

: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo[5].

 

Jagora: Ɗiyar Arju nit taho gani,

: Yau ga ni ga Dela da ni da yarana. X2

   ‘Y/Amshi: Yau ga ni ga Dela da ni da yarana,

: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

     Jagora: Ta shiri tuwo da kyawo,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo,

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

Jagora: Tuwon Rakkiya tuwo ne,

‘Y/Amshi: Wannan na ci shi lahiya nik kwan,

 

Jagora: Na ci tuwon wance nai kasala[6],

‘Y/Amshi: Ran nan ya kwana ɓamɓaraƙ ƙyaure,

: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

Jagora: Kaɗan nika nawa[7] ga tashi,

‘Y/Amshi: Sai ka ga bayan gari ga wandonai.

: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

 

Jagora: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.

‘Y/Amshi: Ta ɗauki yau da gobe,

:  Za ni ganin Ta Ila mai miyat tozo.



[1]  Daddawa.

[2]  Sule da sisi, wato kwabo goma sha biyar.

[3]  Laƙabi ne

[4]  Dokin noma wato wata babbar kyauta.

[5]  Naman tazon sa.

[6]  Rashin haƙuri.

[7]  Daɗewa kafin ya tashi.

Post a Comment

0 Comments