Ticker

6/recent/ticker-posts

Gonar Bakura, Gonar Sardauna Ta Farko

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma 

Gonar Bakura, Gonar Sardauna Ta Farko

Makaɗa Illon Kalgo shi ne babban mawaƙin gonar Sardauna Amadu wadda take a Bakura cikin jihar Zamfara. Wannan waƙar iri biyu ce ya yi a lokuta mabambanta. Ya yi ta farko ‘yar gajera kuma mai amshi daban da ta biyun, a ta farkon cewa yake yi a cikin amshin “Aiki ba ya son ana warganta mai”, amma a ta biyun sai ya ce “Aiki ba ya son ana kwanci banza”. Dukansu dai gonar ya yi wa su, ba kaitsaye Amadu Sardauna ba, sai dai gonar ta shi Sardaunan ce.

Ga waƙoƙin kamar haka:

  G/Waƙa: Gonab Bakura gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son ana warganta mai.

Jagora: Gonab Bakura gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son ana warganta mai.

  ‘Y/ Amshi: Gonab Bakura gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son ana warganta mai.

 

  Jagora: In hwanda maka magana,

: Guda ka bar warganta ta,

: Sa aniya maza

: Ka kama albarkar noma,

: Ashe noma ba,

: Abin wulaƙanci na ba,

: Na gode naAmadu.

  ‘Y/ Amshi: Gonab Bakura gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son ana warganta[1] mai.

 

  Jagora: Abinda yas sa nic ce,

: A kama albarkar gona,

: Zama can nig gani,

: Ga gonas Sardauna,

: Nan ni ishe lamki lamgaɗam,

: Lamkaɗi lamɗam,

: A’a irin huran nono,

: Wadda ad dakakka damamma,

: Hurag ga an tace,

: An zuba tukunya wankaka,

: Huran nan ta kwana,

: Ta yi sanyi bakidai,

: To ashe kai kau ga ka ka jiyo rana,

: Ka shigo cikin inuwar gona,

: A kwalho huran nan,

: Ga kwacciya[2] wata wankakka,

: To a ba ka ka sa hannun dama,

: Ka riƙe shawa zalla,

: Ka kai ta gabaki,

: ka dangana ka riƙe ƙwarya,

: Wuyanka ka ɗora,

: Manƙwatal ƙwantal manƙwal[3],

: Daudu bakinka ka ɗora,

: Murmushi da hwaɗin daɗi,

: Hay ya ce,

: Ya Allah ya kara albarkan noma,

: To zaman noma ba,

: Abin walakanci na ba.

  ‘Y/ Amshi: Gonab Bakura gonas Sardauna,

: Aiki ba ya son ana warganta mai.[1]  Kar a ɗauke shi abin wasa.

[2]  Ƙwarya.

[3]  Tafiyar maƙogwaro sama da ƙasa idan ana shan fura mai daɗi.

Post a Comment

0 Comments