Ticker

6/recent/ticker-posts

Alhaji Garba Dan Ammani

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Alhaji Garba Ɗan Ammani

G/Waƙa: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

.  ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ya gama tashi Garba Ɗan Ammani,

: Sannan ya wuce yag gyara gonar rago.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Abu ya wuce yan nome gonar rago.

  ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Af tashi mu tai gonar Abu Ammani.

  ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Garba mu tai gona Abu Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ga manyan aiki Abu Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Mai mulkin aiki Abu Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Funtuwa birni zani in kwan biyu,

: In ga aiki Garba Ɗan’ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: In je in ga gonag Garba Ɗan’ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: In zai tafi gona bas hi neman rago.

Jagora: Ya wuce wargi Garba Ɗan’ammani,

: Sai aiki Garba Ɗan’ammani,

: In zai tafi gona ba shi neman rago.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora:  In zai tafi gona bas hi neman rago.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ya wuce karta Garba Ɗan Ammani.x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Ba shi dara kigo Abu Ammani.x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: ‘Yag gonakka tsurut gefen hanya,

: .Kak ka gasag Garba Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: ‘Yag gonakka tsurut gefen hanya,

: .Bari gasag Garba Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Bari gasag Garba Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Don‘Yar ekakka dubu da ka samu,

: Bari gasag Garba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Don Ekakka dubu biyu Mamman,

: Bari gasar Garba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Sai ko Hamada garba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Shi gonatai Gaeba sai ka gani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Sunan gonag Garba Sai ka gani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Babu misali babu komai ciki,

: Sunan gonag Garba Sai ka gani.

‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Babu misali ban faɗa ma ƙwarai,

: Gonatai Garba sai ka gani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora:  Taho ka ga gonag garba Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Uban lissafi Garba Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Amman.

Jagora: Sai ko Hamada Garba Ɗan ammani.x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Ina dogar ga Garba Ɗan ammani ,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ina Ɗan Ƙaura Garba Ɗan Ammani,

: Jikan Ƙaura Garba Ɗan Ammani.x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Jikan Ƙaura Garba Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Sannu da aiki Farba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Babban baƙo Garba Ɗan Ammani.x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Amman.x2

Jagora: Sarkin Kukkuri Ummaru,

: Ya san gonag Garba Ɗan’ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Sarki mai Kukkuri Ummaru,

: Ya san gonag Garba Ɗan Ammano,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Shi Ali Kotoko na kai shi,

: Ya san gonag Garba Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ya san gonatai Garba Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Tauraron ‘ya’ya Abu Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ya gama aikinai Abu Ammani,

: Ya koma nome gonar rago,x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Ya taimaki wancan Garba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Kuma agaji wancan Garba  Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Komi zakai Garba Ɗan Ammani,

: Yadda da Allah garba Ɗan ammani.x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Ka yadda da Allah Garba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Tauraron ‘ya’ya Garba Ɗan Ammani, x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Ina Ɗan Ƙaura Garba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Abu jikan Ƙaura Garba  Ɗan Ammani.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Yana nan Funtuwa Garba Ɗan Ammani,x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Da aiki kowane yat taho,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ko hwadawan Garba Ɗan Ammani,

: Shirye da aiki kowane yat taho.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ko da ‘ya’tan  Garba Ɗan Ammani,

: Shirye da aiki kowane yat taho.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Mu nan makaɗanai Garba Ɗan Ammani,

: Shirye da aiki kowane yat taho.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ko da barwan  Garba Ɗan Ammani,

: Shirye da aiki kowane yat taho.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ko malamman  Garba Ɗan Ammani,

: Shirye da aiki kowane yat taho.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: In gode Garba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Tauraron ‘ya’ya  Garba Ɗan Ammani,x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Yara ku kimtsa don abu ya iso,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Manoma kui sabra[1] don aiki,

; Yara ku kimtsa don Abu ya iso.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2

Jagora: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Lebura ‘yan aiki gonatai,

: Tashi ku shirya don Abu ya iso.

‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Tashi ku shirya don Abu ya iso.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ɗan kwadago[2] mai noma a gonar abu,

: Yara ku shirya don Abu ya iso.

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ku tashi ku kama don Abu ya iso,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ya san noma garba Ɗan ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Don ko karatun aiki yai Abu Ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Ya san noma Garba Ɗan ammani,

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.

Jagora: Karatun aiki yai Abu Ammani,x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da aiki Garba Ɗan Ammani.x2[1]  Gonakinsu na noma waɗanda ba a sami gyaeawa ba.

[2]  Mutumen da ake ɗauka a say a yi aiki don a biya shi.

Post a Comment

0 Comments