Salihu Mai Buhu

    Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Salihu Mai Buhu

     G/ WaÆ™a: Mazan jiran damana sale,

    : Salihu Maibuhu, Sale jan zaki.

     

      Jagora: Ai noman dawa ne ga jan zaki,

    : Salihu Maibuhu Sale jan zaki,

    : Dodo mai kuÉ—i,

    : Mazan jiran damana Sale

    : Salihu Maibuhu Sale janzaki.

     

      Jagora : Ai Gyalange akwai manoman da,

    : Amma ba kamas Sale ÆŠan Mamman,

    : Salihu Maibuhu maigidana ne,

    : Gayari akwai manoman da yay yaÉ—a,

    : Amma ba kamas Sale ÆŠan Mamman,

    : Salihu Maibuhu maigidana ne.

     

      Jagora : Tambuwal akwai manoman biÉ—ad dawa,

    : Amma ba kamas Sale ÆŠan Mamman,

    : Salihu maibuhu maigidana ne,

    : Ai Salihu Maibuhu maigidana,

    : Daji ba kasada mai bada mamaki,

    : Mai noman dawa bai ga rana ba,

    : Ai na sanya matan gidan Sale,

    : Na ce mai gadi ina Sale,

    : Salihu mai buhu na wurin aiki.

     

     Jagora : Ku kai mu ga gonar Sale Jan zaki,

    : Ketare godabe[1] Yamma tai dai-dai,

    : Ko ba tambaya kig ga gonatai,

    : In dai kig ga gonasshi ke gane,

    : Ai tsattsaf wuri babu gona kamar ta shi,

    : Ƙi gudu sa gudu sale jan zaki,

    : Mai noman dawa ne da labara,

    : Na dai roƙi sarkin da as sarki,

    : Malikil mulki Lillahi ya  ba ni,

    : Man tasha’u Lillahi na roÆ™a,

    : Sarkin nan da ba’a san zaginai ba,

    : Sarkin nan da bai mantuwa ba ne,

    : Bai haihwa ba,

    : Balle a haihe shi.

    : Bai yara ba,

    : Balle a yare shi.

     

    Jagora : Malikil mulki mai magani Allah,

    : Sarkin jinƙai ruwa inda bayi nai,

    : Allah ka taimaki mai buhu sale Jan zaki,

    : Ai ka bashi abinda duk Sale yan nema,

    : Gumu munata guga da É—anlisu[2],

    : Ni daga wanga burtattki dangi.



    [1]  Titi/hanya.

    [2]  SheÉ—an kenan wanda yakan shagaltar da mutane.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.