Ticker

6/recent/ticker-posts

Dutcin Hwashin Kuyye

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Dutcin Hwashin Kuyye

  G/Waƙa: Ba ya jin rana,

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

  Jagora: Dutcin hwashin kuyye.

‘Y/ Amshi: Ya saba yini dawa ko babu ruwa.

Jagora: Dutcin hwashin kuyye.

‘Y/ Amshi: Ya saba yini dawa ko babu ruwa.

: Ba ya jin rana,

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

Jagora: Hay yau yana gona.

‘Y/ Amshi: Ko can har yanzu bai san ya gaji ba.

Jagora: Ɗan mutanen Ayu.

: Mamman ɗan mutanen Ayyu.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

Jagora: Mamman ɗan mutanen Ayyu.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

Jagora: Mamman ɗan mutanen Ayyu.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

Jagora: Ni dai  ba ni son raggo.

‘Y/ Amshi: Ko danginai suna kuka da shiya,

: Ba ya jin rana,

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

Jagora: Ni dai  ba ni son raggo.

‘Y/ Amshi: Ko danginai suna kuka da shiya.

Jagora: In dai ka ishe gabje,

: Da batcakura sun game mik kaika ciki.

‘Y/ Amshi: In kana ƙauna ta ka taho,

: Ga naira ashirin inji Chiroma,

: Kai ga naira ashirin inji Chiroman Dabai,

: Sama’ila chiroman Dabai.

 Jagora: Nagode Chiroman Dabai.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

  Jagora: Na gode Chiroman Dabai.

 ‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

  Jagora: Mamman Chiroman Dabai.

 ‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

  Jagora: Malam Chiroman Dabai.

 ‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man,

: Ba ya jin rana,

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

Jagora: Ni dai  ba ni son raggo.

  ‘Y/ Amshi: Ko danginai suna kuka da shiya,

: In dai ka ishe gabje,

: Da batcakura sun game mik kaika ciki,

: Insa ka taso a ciki,

: Ga nera ashirin inji Chiroman,

: Hei ga nera ashirin inji Chiroma,

: Chiroman Dabai Sama’ila,

: Chiroman Dabai yace a kawo maka.

Jagora: Na gode Chiroman Dabai.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

Jagora: Na gode Chiroman Dabai.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

Jagora: Mamman Chiroman Dabai.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

Jagora: Malam Chiroman Dabai.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man,

: Ba ya jin rana,

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

Jagora: Ni dai  ba ni son raggo.

‘Y/ Amshi: Ko danginai suna kuka da shiya.

Jagora: In dai ka ishe gabje,

: Da batcakura sun game mik kaika ciki?

‘Y/ Amshi: Ba ya jin rana,

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

Jagora: Ina Ɗan’ali Dabai.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kun ka yi man,

: Tunda kiɗin noma ne,

: Baya jin rana,

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

Jagora: Zarton hwashin kuyye.

‘Y/ Amshi: Ya saba yini dawa ko babu ruwa.

: Ba ya jin rana,

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

Jagora: Ni dai  ba ni son raggo.

‘Y/ Amshi: Ko danginai suna kuka da shiya.

Jagora: In dai ka ishe gabje,

: Da batcakura[1] sun game mik kai ka ciki?

‘Y/ Amshi: In sa kiran tun kan ka fito.

Jagora: Na gode girman wanzanmai,

: In dai gyara akai man su ka yi man.

: In aski akai man su ka yi man.

: Wallai ko kaciya su sunka yi man,

: Kowag girma ba yanka.

‘Y/ Amshi: Mai sulli[2] ba’a sa hannun da shiya

: Ba ya jin rana

: Irin Sule sai duhu Tonka ya taho.

Jagora: Na gode girman wanzanmai

: In dai gyara ake man ku ka yi man.

: In aski akai man ku ka yi man,

: Wallai

‘Y/ Amshi: Ko kaciya su sunka yi man.

Jagora: Ali na gode ma.

‘Y/ Amshi: Ban rena ba kyauta kunka yi man.

Jagora: Malam Ali na gode ma.

[1]  Wasu ciyayi ne masu wuyar sha’ani, waɗanda manoma ke daga da su wajen noma.

[2]  Wanda ba a yi wa kaciya ba, sai dai ya sa zobe ya tattare loɓar.

Post a Comment

0 Comments