Ticker

6/recent/ticker-posts

Sun Zaɓi Su 'Yanta Kansu

Saran reshe da adda,

Mai saran na samansa.


Ba bukatar ai bayani,

Ganganci ne da hauka.


Wauta ce babu shakka,

Yin gaggawa a salla.


Ƙarshe sallar ta ɓaci,

Kowa ya rasa a taɓe.


Duk Limami na gaske,

Bai gaggawa a jam'i.


Nutsuwa matsayi gare ta,

Cikin sallar farilla.


Farilla ce ga Liman,

Ba'adi ƙabali ya sansu.


Direba da ke da saiti,

Samsam bai take mota.


Bare motar da babu,

Birki a take totur?


Mulkin jama'a a kullum,

Amana ce ta wajib.


Shugaban na ƙasa da gwamna,

Kar su kai jama'a mayanka.


Yaƙi wallahi Allah,

Masifa ce ƙazama.


Bare a cikin gidanka,

Wa zai so ban da gaula.


Gaskiya ne shi na rami,

Ko takobi sai ya kama.


Maƙota 'yan uwanmu,

Sun jima sosai a rami.


Sun zaɓi su 'yanta kansu,

Me ye matsalar faɗe ta.


Tunda mu bauta mu ke,

Mu bar su su shaƙi iska.


Dukiya ta ma'adanansu,

Su amfana da kansu.


Kanzagin sai sun ta bauta,

Gaskiya ba na mu ne ba.


Mu dai da muke ta bacci,

Hakan muka sowa kanmu.


Mu rayu mari ƙafarmu,

Sai mu farka 'yan uwa.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments