Batun Miji Ya Fara Gaida Matarsa

    Wannan batu ya samo fantsuwa ne daga shirin MATA A YAU inda ya jawo ka-ce-na-ce a dandalolin sada zumunta har ta kai wasu na kafa hujja da karatun Malam Daurawa. Shi ne nake ƙoƙarin jan hankalinsu cewa:

    Wannan zagayawa na gaisuwa da Ya Sheik yake mana nuni Manzo SAWS ya yi, ba fa da mutum mai mace ɗaya ake nufi ba. Wannan al'amari ana nufin magidanci mai mata biyu ko uku ko huɗu abin ya shafa 😅😂🤣

    In matar mutum ɗaya to zagayawa ganin ya kowacce take bai taso ba. In kun tashi a ɗaki ɗaya turakarka ko ɗakinta wa zai fara gaida ɗayan? Ba ƙarami ne shari'a ta ce ya fara gaida babba ba? Miji shi ne babba a tsarin auratayya.

    In matarka guda jallin jal kamar idon Vespa ga shi ta hana ka ƙara aure 😆 sai a ce kuma kullum da safe ta karage ka zo ka yi mata sallama sannan ka tsugunna ka gaishe ta "Ina kwana?" Hakan za ta yiwu kuwa? Ba haka ake nufin Annabi SAWS ya yi ba fa.

    Aatoh kar mata su miƙe ƙafafuwansu su ce yin haka sunnah ce. Manzo ASWS duba kowacce daga matansa yake yi daga bisani yayi y'ar hira da ita yana tambayar lafiyarta, walwalarta, natsuwarta, bukatunta da dai sauransu.

    RasululLaah SAWS ya kan je É—akin kowacce ya yi hakan ne don gudun rikicinsu in aka ce kowacce ta je wajensa ta gaida shi. Kar wacca kwananta ne a cikinsu ta ce an hana ta sakewa da mijinta ana ci mata lokaci.

    Ka san mata da kishi za ta yiwu in suka yi gamo a turakarsa ba abin mamaki ba ne faÉ—a ya kaure a tsakaninsu ko a samu su dinga yiwa juna habaici, gugar zana, tsokana da makamantansu a kulli yaumin.

    Saboda haka don gudun rikicinsu ya sa Manzo SAWS ya kan je ya duba kowaccensu a É—akinta. Ba zuwa gaishe su yake yi kamar yadda muka san gaisuwa irin tamu ta al'ada ko yadda muka É—auki gaisuwar gargajiya yake yi ba.

    Zuwa duba su yake yi. Dubiya kuwa daban gaisuwa ina kwana ina wuni barka da dare daban don haka kar mu É—auka abun da ake nufi ke nan. Kuma in ya je musu SAWS ya kan shiga ne da sallama wacca gaisuwa ce da addu'a ma

    A fahimtar wasu samsam ba zuwa gaishe su don isarsu da jijji da kansu ake nufi ba. Sallama yake yi musu sannan ya tambayi kowacce ya suka kwana ya suka yini da fatan ba su da wata damuwa.

    Wai shin ba mace ba ce aka ce da za a bari mutum ya yiwa wani ɗan Adam sujada a addinin Islama da mace ce za a ce ta yiwa mijinta haka ba don tsananin haƙƙinsa dake kanta ba? Kuma sai a wayi gari wasu tsirarun mata su ce miji ne zai dinga zuwa gaida da su harda wani fakewa da hadisi?

    Gaisuwar girmamawa daban wacca ita ake nufi a nan mace ta yiwa mijinta wacca kuma matan suke so miji ne zai dinga yiwa matarsa alhali kuwa mai yiwuwa saboda butulci ma ba ta cancanci ko kula ta ya yi ba balle ya yi mata wannan tagomashin ba.

    Ehe, kowa ya gane don tabbas fahimta fuska kowa da tasa amma gaskiya kuwa É—aya ce.

    Abin nema dai anan shi ne in miji ya je wa matarsa ya yi mata sallama "Assalamu alaikhi." wacca gaisuwa ce irin ta addinin Musulunci. Sai ta amsa masa da "Wa alaikassalaam". Amsawar kuwa wajibi ne.

    In ya shiga ɗakinta ya zauna ita kuma matar sai ta yi masa gaisuwa ta al'adarmu wato ta sauko daga abin zamanta ta tsuguna a gabansa ta ce da shi "Yallaɓai ina kwana?" ko "Ina wuni?" ko "Barka da dare?" 😀

    Ba shike nan an wuce wajen ba? Amma ka zo ka yi sallama an ƙi a amsa maka balle a gaida ka ina kwana ba dole ka yi bambami ko ka yi barazana ta da zaune tsaye ba! 😅 Kowa ya kwana lafiya aka ce shi ya so ko?

    Daga ƙarshe dai kira za mu yi ga mazaje da matayenmu don Allaah kowa ya dinga kai zuciyarsa nesa. A dinga haƙuri da juna sannan a nemi ilimin zaman aure. Don wAllaahi azimu ba da ka ake yinsa ba.

    Komai za ka yi ko za ki yi ku tambayi kanku "A irin wannan al'amari ko yanayin rayuwa ya Manzon Allaah SAWS ya yi? Sai ku bincikoa Qur'ani da Hadisi ku kwaikwaye shi sau da kafa in sha Allaah ba za ku ga nadama ba.

    Daga Taskar

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +234 806 706 2960

    A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.