Ticker

6/recent/ticker-posts

Har Yanzu Dai A Kan Batun Mata Ta Fara Gaida Mijinta

Addinin Islama rayuwa ce cikakkiya wacca yin komai da aka sani yana kan tsari, ka'ida da dokoki da suka samo tushe da asali daga Al-Qur'ani da Sunnar Manzo SAWS.

In ka ga mutum namiji ko mace suna tafka shirme ko kuskure a wajen furta wata magana ko yin wani abu a rayuwarsu to ka tabbatar sun jahilci al'amarin. Shi yasa Allaah SWT Ya ce da mu "Iqra'" wato mu yi karatu mu nemi ilimi.

Don samsam ba hankali a ce mutum mai ilimin Shari'a ya zo ya yi maka sallama wato ya cika umarnin Allaah da Mazonsa na baka haƙƙinka kai kuma ka gaza amsawa, abinda ya zama wajibi ne akanka ka amsa masa sallamar nan.

Sallama kuwa ba zan ce dukkanmu ba don ba kowa ne yake da ilimin addini ba amma da yawanmu mun san gaisuwa ce kamar yadda malamai kan ce irin ta addinin Musulunci.

Don haka da aka ce Annabi SAWS yana shiga ɗakin matansa yana yi musu sallama (gaisuwa) ba irin tamu gaisuwa ta "Ina kwana?" ake nufi kai tsaye ba. Sallama ta addinin Islama ake nufi wanda kowa ma za ka yi masa.

Sannan Manzo ASWS ya kan yi hakanne don bin doka da ka'ida da koyarwa tunda mun sani a tsarin gaisuwa matafiyi ne ke wa na gida sallama na tsaye shi ke wa na zaune sallama na zaune ke wa na kwance sallama dds.

A shari'ance in har al'ada ba ta saɓawa hukuncin Al-Qur'ani da Sunnar Manzo ba to akan bar ta ba a dakile ta. Miji tunda shi ne shugaba a gidansa ai hankali ne duk inda ya gamu da waɗanda suke ƙarƙashinsa su fara gaida shi.

Matar mutum a ƙarƙashin mulkinsa take don haka in ya zo ya yi mata sallama to wajibi ne ta amsa masa. Bayan ta amsa ta kuma ɗora masa da murmushi, godiya, kyautatawa, rusunawa da ƙanƙan da kai.

Wato ta nuna yaba ƙoƙarinsa na samar mata da wasu abubuwan gudanar da rayuwa. Kar mu manta Allaah AWJ Ya ce in aka yi maka sallama ka maida kwatankwacin ta ko ka ɗora akan ta da wa rahamatullah wa barakatuhu ko?

Ba saɓanin haka ba. Shi ya sa aure da yawa ke mutuwa saboda rashin iya godiya ga miji ko ga matar wanda Allaah SWT Ya ce in mutum ya iya godiya sai Ubangijinsa Ya ƙara masa daga alkhairinSa.

Gaskiya akwai rashin sani rashin ilimi da rashin sanin ya kamata a cikin wannan al'amari na kawo zancen nan cikin shirin Mata A Yau don a haƙiƙanin gaskiya ba abu ne da za a ce an kawo shi bainar jama'a haka ba.

Daga Taskar

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960

A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments