Ticker

6/recent/ticker-posts

Mata Ta Gari Ke Gai Da Mijinta Ina Kwana

1.

Mata ta gari ce ke tashin miji

Da asubahin fari ya sallaci Mai'giji

Ta sa masa ruwan dumi babu turji

Ya yi wanka da alwala yana mai ji

Da ita a zuciyarsa ba tare da tababa ba.

2.

Kan ya dawo ta dafa masa shayi

Na so da ƙauna ba ta wani shayi

Zabinta ne daga maza dubu a layi

'Da ba bawa ba daga cikin wasu bayi

Na Ilahun sammai da ƙassai Ya Rabba.


3.

Ya ce "Salamun alaikhi ya ukhtiy"

Ta ce "Wa alaikassalaam ya Abti

Sannu da zuwa bugun zuciyar Ati

Hasken ruhinta wanda ba ya latti

Wa ya ce ba da bazarka nake rawa ba?


4.

Zinari ka fi azurfa balle tagulla

A duwatsu ina wanda yai ya Dala

Gogana ka fi kowa ko a karin hula

Kar fa a nemi masu wasa da Dala

Ga ni gabanka durƙushe da kuɗin Laraba.


5.

Wasu na zuga ni kar in gaida ka

Burinsu ne in raina ka in sauya ka

Alhali a gida an ce in girmama ka

Ta su zan bi ko Manzo Nabiyyinka

Ina masu hankali ku zo ku taya ni dubawa.


6.

Tunda kai sallama mijina ka fita

Amsa maka sai na nuna bajinta

Tabbas zan yiwa kafarka tausata

Da Zaitun na farko daga zuciyata

Suna so ba sa so ni dai ban ga ta zama ba.


7.

So suke a kama ƙirga mun maza

Zakaru biyar sai ka ce wata kaza

Ni ke nan kamar kalwa an baza

A kasuwar ƙauye ƙudaje na gabza

Ku bar ni in ɗau alJannata inda ba musu ba.


8.

Wata ta ce wai mijinta waye shi

A matsayi har ya isa ta gaishe shi

Ni kuwa na ce "Ni nawa shi ne shi

Da nake burin Allah Ya rahamshe shi

Yai masa hisabi ba tare da wani bincike ba."


9.

Ya ku matanmu ku fa sani a yau

Rayuwan nan cike fa take da hau

Mu kiyayi Shaiɗan don zama lau

Ya ishe mu izina ƙunar ranar rau

Ba sai mun tsinci kanmu cikin da na sani ba.


10. 

Waƙa ce sabuwa fil cike da kashedi

Ta Ahamadu ɗan Tijjani mai muradi

A bar fitina du mu kiyayi yaɗa fasadi

Kar gidanmu asa su Walakiri yin gadi

Gobe kiyama Allah sada mu da ɗan Suwaiba

Daga Taskar

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960

A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments