Ban Yi Zato Ba

    1.
    Kai na sanya farko,
    Ya Rabbi Sarkin iko,
    Kai nake yuwa roko,
    Burina Kai amsawa.

    2.
    A kwanaki na nuna,
    Nai batu kan k'auna,
    Ina ganin za ku tuna,
    Firdausi nai magantuwa.

    3.
    Yau duk jiki ba lafiya,
    Bana iya yin har tafiya,
    Ga Magani na had'iya,
    Idan da rai da rayuwa.

    4.
    'Yar Kazaure ce yarinya,
    Da ita nake yin tutiyya,
    Son ta ya shiga zuciya,
    Yau ina cikin damuwa.

    5.
    Da sonta ni nai a niya,
    Firdausi gata da tarbiya,
    Ga zuciya tai mamaya,
    Firdausi ba ta da rowa.

    6.
    Kullum idan nai kiranta,
    Wallahi ban samunta,
    Wannan yasa na rikita,
    Na ka sa duk ganewa.

    7.
    Wasu cikin danginta,
    A ciki akwai yayarta,
    Har da k'anin babarta,
    Ke hure mata kunnuwa.

    8.
    Firdausi gata Kazaure,
    Can baya duk ta jure,
    Guiwarta yau ta sare,
    K'auna ta fara gazawa.

    9.
    Sune suke mata lecture,
    Suna 6ata mata future,
    Ni dai ina kan juncture,
    Da ilimu nake haskawa.

    10.
    Firdausi 'yar masu kudi,
    Gidan su ga shi da fad'i,
    Burinta ta yi mini tad'i
    Dan nai nishadantuwa.

    11.
    To dama ina yin sana'a,
    Ta littatafai da jama'a,
    A kanta na samu sa'a,
    Ni Aliyu tai haskakawa.

    12.
    Ni kullum ita ce burina,
    Dan na samu na kaina,
    Domin na rike dangina,
    Sana'a na ke jarrabawa.

    13.
    Amma ni na yi karatu,
    Na yo N C E na bautu,
    Har da digiri na wahaltu,
    Ina kusa da kammalawa.

    14.
    Da littatafai nai rubutu,
    Dan d'alibai sui ingantu,
    Da wak'ok'ina a nazartu,
    Ubangiji ya mini baiwa.

    15.
    Na karaya yau na rasa,
    Ni Firdausi tai min nisa,
    Cikin maganar ba wasa,
    Da Firdausi mun rabuwa.

    16.
    Na yar da da ikon Allah,
    Sarkin da ba shi kasala,
    Aurenmu idan ya yi sila,
    Wallahi ba mai togewa.


    (C)Aliyu Idris
    (Sarkin Yaƙin Malumma)
    19/08/2023

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.