Ticker

6/recent/ticker-posts

Laƙada Raliyallahu

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Laƙada Raliyallahu

Jagora: Laƙada raliyallahu anal muminina,

 Amshi: To

Jagora: Angal lahu angaruhin mu’asha,

 Amshi: To

Jagora: An aiko mu inda malam mu gan shi,

 Amshi: To

Jagora: Ga shi biki gare shi mi zamu ba shi,

 Amshi: To

Jagora: Kai ka mukai mu samu lada cikakka.

 Amshi: To

 Jagora: Ladar nan ta gobe ranar ƙiyama,

Amshi: To

Jagora: Je ki marowaci ka sake dubara,

 Amshi: To

 Jagora: Ranar lahira kana ci da kuka.

 Amshi: To

 Jagora: Kai kukan jini ka koma na tilas,

 Amshi: To

Jagora: Ba ka da ɗan ƙane bare ɗan aboki.

 Amshi: To

Jagora: Inna in sallah ki kai ki ɗauro da niyya,

 Amshi: To

Jagora: In Azumi ki kai ki ɗauro da niyya,

 Amshi: To

Jagora: In zakka ki kai ki ɗauro da niyya,

 Amshi: To

 Jagora: In tsalki ki kai ki ɗauro da niyya,

 Amshi: To

 Jagora: Ba tsalkin ruwa ba tsalkin ibada,

 Amshi: To

Jagora: Tsalkin zuciya gaba ɗai da sunnah,

 Amshi: To


Post a Comment

0 Comments