Ticker

6/recent/ticker-posts

Babi Na Farko - Zababbun Wakokin Mawakan Baka Na Noma

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Babi Na Farko - Waƙoƙin Da Mawaƙan Noma Suka Yi Wa Manoma

 

A wannan babin za a kawo wasu waƙoƙin ne waɗanda waɗansu makaɗan da aka san su a matsayin makaɗan noma a yankin ƙasar Hausa suka yi wa manoma domin su ƙara harzuƙa su wajen noma. Akwai mawaƙa da dama da suka yi fice ta wannan haujin a al’ummar Hausawa, waɗanda suka yi waƙoƙinsu ga wasu mutane waɗanda suka shahara ga aikin gona, wato noma na duƙe, wannan da Hausawa suke yi wa kirari da “Noma na duƙe tsohon ciniki, kowaz zaka duniya kai ya tarar”.

 

Daga cikin irin waɗannan mawaƙan akwai Daudun kiɗi Jambaƙo da Baƙo Rugum Ƙiri da Abdullahi Ɗanɓurji Morai. Haka kuma akwai kallabi tsakanin rawunna wato Hauwa Kulu Mukkunu.

 

Kamar yadda na faɗa a cikin gabatarwar wannan aikin cewa akwai makaɗa da dama waɗanda suka yi waƙoƙin noma, ko kiɗe-kiɗen noma waɗanda hannunna bai sami kai wa ga waƙoƙin nasu ba, ko kuma waɗansu waƙoƙin da muka kasa fahimtar kalmomin da ke cikinsu, kamar makaɗa Garba Ɗanduddu Gangarak Kuryad Dambo da makaɗa Hamza Satiru waɗanda su ma shahararrun mawaƙan noma ne, kuma in Allah ya so nan gaba ina da nufin in ƙara yunƙuri in nemo su domin daɓena ya ji makuba. Haka kuma wasu makaɗan noman kiɗi ne wato tafashen noma kawai, sai kirari da sukan yi a matsayin waƙoƙin, kamar su makaɗa Atta Dabai da Mande Dalli Bunguɗu da sauransu. Don haka sai a yi haƙuri a matsayina na ƙaramin manazarci, na kasa samun hanyar da zan kawo su ta yadda za a fahimce su sosai da sosai, Ina ba irin waɗannan makaɗan haƙuri, su kuma al’umma da ɗaliban ilmi mazartra sai su yi mani uzuri su karɓi ɗan abin da ya sawwaƙa.

 

Akwai hoto ku hotunan mawaƙan tare da ɗan taƙaitaccen tarihinsu kafin a kawo waƙoƙinsu domin a san su, sannan a yi amfani da waƙoƙin nasu. Da fatan Allah ya taimake mu, amin.

Post a Comment

0 Comments