Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
1.1 Waƙoƙin Noma Na Makaɗa Daudun Kiɗi Janbaƙo
Ummaru
Daudun kiɗi makaɗin noma ne wanda yake
amfani da gangar noma wato irin wannan da ake kira ta guiwa ko tallabe wajen kiɗinsa na noma.
1.1.1 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Daudun Kiɗi Janbaƙo
An
haifi Daudun kiɗi a wata anguwa da
ake kira Ɗanhili a garin Janbaƙo, cikin ƙaramar hukumar mulkin
Maradun ta jahar Zamfara. Sunansa shi ne Ummaru, sunan mahaifinsa Ibrahim wanda
ake kira Makaɗa Ibrahim Janbaƙo, wato dai Daudun kiɗi ya gadi kiɗi ne ga mahaifinsa
Ibrahim duk da yake bai yi kiɗi tare da mahaifinsa ba.
Daudun kiɗi Janbaƙo ya fara kiɗi da waƙa ne bayan rasuwar mahaifinsa Makaɗa Ibrahim. Bayan rasuwar mahaifin nasu sai yayansa wanda ake kira Dogo ya jagoranci tawagar kiɗin wanda Ummaru ya kasance yana ɗaya daga cikin yaransa. Haka ya yi ta biyar yayansa Dogo har Allah ya yi masa rasuwa. Bayan rasuwar yayansa ne sai shi ma ya ɗauki nashi matsayi na sana’ar kiɗi da waƙa a matsayin mai cin gashin kansa.
Daudun kiɗi Janbaƙo ya fara kiɗi ne a garin Janbaƙo yana yi ma wasu mutane kamar sarkin Janbaƙo da wasu. Amma waƙarsa ta farko da ya yi a wajen garin Janbaƙo, ya yi ta ne a garin Dosara da ke ƙaranar hukumar mulkin Maradun, kuma ya yi ma wani mutum mai sana’ar gini wanda ake kira ‘Musa magini’ Shi Musa magini shi ne ya gayyaci Daudun kiɗa domin ya yi masa waƙar gini a lokacin da ana ginin gidan Sarkin rafin Dosara. Babban wakili giye Janbako, kuma Daudun kiɗi ya karɓa wannan gayyata inda ya je ya yi masa waƙar gini wadda da wanan waƙar ce ta Musa magini Dosara Daudun kiɗi ya fara shahara har sunansa ya yi fice.
Bayan dawowar Daudun kiɗi daga wannan gayyata da Musa magini ya yi masa a garin Dosara ne ya canja shawarar komawa kiɗin Noma baki ɗaya wanda daga nan ne ya sauya akalar sana’ar kiɗinsa da waƙa zuwa kiɗin Noma waƙa ga manoma na garin Janbaƙo.
Alhaji Umaru (Daudun kiɗi Janbaƙo) ya fara yi ma wani mutum da ake kira Altine’ waƙar noma a garin Janbaƙo kuma da wannan waƙar ce ya fara fice a fagen waƙar Noma.Wannan ya sa duk za a yi wani taro na noma kamar noman gandun sarki to Daudun kiɗi ne ake kira ya gabatar da waƙarsa. Haka kuma daga wannan waƙar ta Altine da ya fara ne ya yanke shawar shiga waƙar noma gadan-gadan.
Waƙarsa ta biyu (2) wadda ta ƙara bayyanar da shi ita ce waƙar da ya yi wa wani mutum da ake kira Maidamma na Ladi mutumen wani ƙauye ne da ake kira “Tungar na yar ciga” tsakanin Janbaƙo da Faru. Wannan waƙa ta “Maidamma Na Ladi” ta taimka ƙwarai wajen mutane su san Daudun kiɗi Janbaƙo ,ba’a garin Janbaƙo kawai ba, har da ƙauyukanta da wasu manyan garuruwa da suke maƙwabtaka da Janbaƙo.
A taƙaice dai Daudun kiɗi ya yi waƙoƙi da dama amma fitattu daga ciki kamar yadda yaronsa Iliya ya ce su ne guda ashirin da tara (29), daga cikin waƙoƙin, waƙoƙi goma sha takwas (18) ne ya yi a Garin Janbaƙo ga mazauna garin Janbaƙo. Daga cikin shahararrun waƙoƙinsa akwai ta Ɗan Maliki da sarkin fada duk a garin Janbaƙo, Sai kuma waƙar Alhaji Garba Dauran a wajen Janbaƙo.
Allah mai yadda ya so! Daudun kiɗi Janbaƙo ya tuba ya bar sana’ar kiɗi da waƙa bayan ƙaddamar da shari’ar Musulunci a Jahar Zamfara a shekarar dubu biyu (2000). Amma kafin ya bar sana’ar kiɗi da waƙa wato lokacin da yana waƙa yana da yara Shida (6) Daga cikinsu akwai Iliyasu wanda shi ne babban yaron Daudun kiɗi, sai Sa’adu da Yunusa da Sani da Abdul-karim sai kuma Ɗahiru.
Bayan tuba da barin kiɗan da Makaɗa Ummaru Ibrahim (Daudun kiɗi Janbaƙo) ya yi sai ya ƙirƙiri Makarantar Allo inda ya ke koyar da Almajirai na gida da wasu da ake kawowa daga ƙauyuka don karatun alƙur’ani. Kuma a bisa wannan hanyar ne Allah maɗaukakin sarki ya karɓi rayuwarsa. Kasancewar ko kafin Daudun kiɗi ya fara waƙa shi Almajiri ne ya yi karatun addini na almajiranci.
Komai ya yi farko sai ya yi ƙarshe in banda ikon Allah, don haka Mallam Umar Ibrahim (Daudun kiɗi) ya rasu a tsakanin shekarar dubu biyu da biyar ko ta dunu biyu da shida 2005/2006 a garin Janbaƙo a shiyar Ɗanhili. Ya rasu ya bar Matan Aure biyu da ‘ya’ya goma sha Ɗaya, Maza biyar (5) Mata shida (6) daga cikin Maza sun haɗa da Rabi’u da Sama’ila da Basharu da Aliyu da Jamilu sai kuma Mata akwai Ladi da Rabi da Rakkiya da Salamatu da Saude da Ruƙayya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.