Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin La'asar Ya Yi Ban Sami Damar Yi Ba Har Haila Ta Zo Mini

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

السلام عليكم

Mutum ne tafiya ta same shi zuwa wani gari, to sha'anin mota har lokacin sallar La'asar bai sami damar yi ba har magriba ta yi, to a tsakanin wannan lokacin sai ga jinin al'ada ya taho, ya matsayin wannan sallar tasa ta La'asar ɗin kenan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

وعليكم السلام

To 'yar uwa wanda ta sami kanta a irin wannan hali, za ta rama wannan sallar La'asar ɗin da ba ta sami damar yi ba bayan ta yi tsarki, saboda lokacin sallar ya yi kafin hailar tata ta zo mata ne, har ma sai bayan lokacin La'asar ya fita sannan hailar ta zo mata, don haka ne hukuncinta ya zama za ta rama .

Amma ba za ta rama sallar Magriba ba, tun da a daidai lokacinsa ne hailar ta zo mata.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐓𝐄𝐋𝐄��𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments