Ticker

6/recent/ticker-posts

Zubin Ɗiya

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Zubin Ɗiya

Wannan na nufin yadda zaren tunanin mawaƙi ke bayyana a cikin ɗiyan waƙar da yake tsarawa. Wato zuwan saƙon waƙa bi da bi ba tare da rikita tunanin mai saurare ba. Waƙoƙin bara suna tafiya bisa irin wannan zubi. Wato saƙon cikinsu yana fitowa a tsare ba tare da kwan gaba kwan baya ba. Misali:

Jagora: Sai ni na malam Sani.

 Amshi: To.

 Jagora: Almajiri da ƙaho.

 Amshi: To

 Jagora: Guda na shukar gero

 Amshi: To.

 Jagora: Guda na shukar dawa.

Amshi: To.

 Jagora: Guda na shukar marar tuwo.

 Amshi: To.

Ja gora: A sa ta a baki da daɗi.

 Amshi: To.

 (Almajiri da Ƙaho)

Wannan waƙar an tsara ɗiyanta daki-daki daidai yadda tsarin tunanin mawaƙin yake. Idan aka lura waƙar kamar ta kamanci ce, wato nuna wata jaruntaka amma ga abinci. Tun a ɗa na farko a ka fara da kirari na cewa shi na Malam Sani ne kuma ƙahoni gare shi. Daga nan sai ya fara bayyana aikin kowane ƙaho daga cikin ƙahonin. Ƙaho biyu na farko na aiki ne, wato shuka ta gero da dawa. Ƙaho na uku kuwa nasukar marar tuwao ne. Ka ga ya tsara zubin ɗiyan waƙarsa daidai da zaren tunaninsa na son bayar da nishaɗi ga masu saurarensa. Ya far da aiki domin a ji kamar dukan ƙahonin wani abin kirki suke yi. Bayan hankalin masu saurare ya tafi a haka, sai kuma ya waske da cewa ɗaya ƙahon na cin tuwo ne. Wannan zai sa masu saurare dariya, kuma ita ce manufar.


Post a Comment

0 Comments