Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Ƙaramin Turken Turanci a Waƙoƙin Amali Sububu
Turanci harshe na mutanen Turai
wanda Turawa suka shigo da shi a ƙasarmu Nijeriya,
ana samunsa ne ta hanyar boko. Amali ya kawo waɗansu
kalmomin Turanci a ciki waƙoƙinsa kamar haka:
Jagora : Mun kwana munka yo sallah munka
: dawo,
: Amali na yi hul tanki[1]
tun da sahe,
: Ni dai ina ta ɗora giya babu dama,
: Mun zo Arewa mun
yi kwana,
: Munka kwan nan.
’Y/Amshi : Jijjihi yakai daji baya wargi[2],
: Kodayaushe shi
dai baiu san sake ba,
: In yi mai kiɗin aiki Garba Dauran.
(Amali Sububu: Garba Dauran)
Hul tanki a nan yana nufin cika tankin wani abin hawa da
mai “wato full-tank” kamar mashin ko mota da sauran injinonin da ke amfani da
mai. Ita kuma kalmar “kwana” da Amali ya yi amfani da ita ararriya ce daga
Turanci wato “corner” wadda take nufin juyowa ko sake hanya daga wadda mutum
yake a kanta tun farko.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.