Ticker

6/recent/ticker-posts

Salon Zayyana A Wakokin Amali Sububu

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Salon Zayyana A Waƙoƙin Amali Sububu

Salon zayyana wani salo ne da mawaƙa kan yi amfani da shi a cikin waƙarsu, inda suke kwararo wasu kalamai waɗanda ke iya nuna a zuciya kamar ga abin nan yana faruwa. Kamar kana tsaye kana kallo. Ga yadda masana suka ce game da ma’anar zayyana:

 

Yahya (2001: 89) Salon zayyana na nufin amfani da kalmomi a cikin waƙa tattare da kalmomin na maganar da suka fito cikinta za su ƙirƙiro siffar abu ko yanayi a cikin zuciyar mai karatu ko mai sauraren waƙar.

 

Kamusun Hausa (2006493) ya bayyana salon zayyana da cewa “Kalmar na nufin ƙawata wani abu: zana sura ko kamannin wani abu.

 

Ɗangambo (2007:44) ya ce salon zayyana na nufin doguwar siffantawa ko hoto cikin bayani.

 

Bunguɗu (2015) cewa ya yi “Wannan salo shi ne wanda mawaƙi kan tsaro bayanin faruwar wani abu, ko yadda zai faru a cikin waƙa ta har yadda mai saurare zai ji kamar ga abin nan a gabansa yana faruwa. Wato bayanin da mawaƙin ya yi ya sa idanun zuciyar mai saurare na ganin yadda abin ke gudana”[1], Ga misalan zayyana da aka tsamo daga cikin ɗiyan waƙoƙin Amali kamar haka:

Jagora : Yunwa ta taho da gorori[2],

: Ta iske maza,duk ƙaton,

: In taƙ ƙumai ga wuya sai,

      : Ya shantala[3],

  ’Y/Amshi : Sai ya hurce Kwantagora.

: Riƙa da gaskiya.

: Noman ba kashi ya kai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama.

 

  Jagora : Sannan ta waiwayo,

  ’Y/Amshi : Ta ga ƙaton ta bai ɗaga ba,

      : Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 

  Jagora : In tak ƙumai[4] bugu,

  ’Y/Amshi : Sai ya kai gabas ga Borno.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

     : Yari ɗan Bagge,

      : Noma ba ya sa ka rama.

 

  Jagora : Kuma sai ta waiwayo,

  ’Y/Amshi : Ta ga ƙaton ta ba ɗaga ba,

      : Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 Jagora : In taƙ ƙirai[5] bugu,

 ’Y/Amshi : Wannan Yamma zaya dosa.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 

  Jagora : Ga hwa gudun muna ta yi,

   ’Y/Amshi : Amma ba a yi Arewa.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

(Amali  Sububu: Yari Ɗan Bagge)

 

A waɗannan ɗiyan waƙar mai saurare zai riƙa gani a cikin ransa kamar ga yunwa nan wata ƙatuwa baƙa, tana riƙe da abin bugunta, tana ta bugun ƙatti, su kuma suna ta gudu suna watsewa ta Gabas da Yamma da Kudu, amma ba a bin ta Arewa saboda a nan take tsaye da kulkinta.

 

Jagora : Ko Hushe mai koko ta sayar,

’Y/Amshi : Ta bam mai na gaskiya,

    : Noma ba kashi yakai ba,  

     : Yan ɗan Bagge,

  : Noma ba ya saka ka rama.

 

Jagora : Masu biredi sun sayat,

 ’Y/Amshi : Sun bam mai na gaske zamne.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama.

 

Jagora : Kuma an taho da tsaba,

: Na iske an sayar,

     ‘Y/Amshi : Dud dai mai na gaske na nan,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama.

 

Jagora : Hashimu ya taho da rogo,

: Na iske ya shigat[6],

’Y/Amshi : Duddai mai na gaske na nan.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge, Noma ba ya saka rama.

 

Jagora : Ko ‘Yat tama da adda haki[7],

    : Na ga ta sayar,

’Y/Amshi : Ta bar mai na gaske zanne,   

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 

Jagora : Malan Abdu ya sayar,

’Y/Amshi : Ya bar mai na gaske zanne.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 

Jagora : Kuci mai yamri[8] ta sayar,

’Y/Amshi : Ta bar mai na gaske zaumne,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,  

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama.

 

Jagora : Kuma Dela uwat[9] tuwo,

: Kuma mun iske ta sayas,

’Y/Amshi : Ta bam mai gaske zamne,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama,

 

Jagora  : Hassi ta Amali ta bugo hwanke,

: Na ga ta sayas,

’Y/Amshi : Ta bar mai na gaske zamne,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama, 

 

Jagora : To ƙarya ba na gaske ne ba x2,

’Y/Amshi : To ƙarya ba na gaske ne ba,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 (Amali  Sububu: Yari Ɗan Bagge)

 

A nan kuma mai sauraren waɗannan ɗiyan waƙar zai iya riyawa a ransa kamar ga mutane nan masu sana’o’i daban-daban a wata ‘yar kasuwar unguwa a garin Hausawa (‘yar yara), duka sun yi sa’ar ciniki duk sun sayar amma dai babu wanda ya zo ga mai nagaske ya saya.

Jagora : Ga sarkin noma za shi[10] gona,

: Ga jaki goma sha biyar ya koro,

: Duk kowane da taki,

: Ga kwando ya ciko da taki,

: Ya ɗauka ya azo ga kai na,

: Ga kalme ya saɓo da gitta,

: Ga kwashe ya riƙo a hannu,

: Ga juji ya laƙo gaba nai,

: Ga juji ya laƙo ga baya,

: Ni dai na dabugo gaba nai,

: Ban san kan inda ya nuhwa ba,

: Kuma nijjirkito shi baya,

: ,Ban san kan inda yan nuhwa ba

: Kuma nij jirkito shi baya,

: Dub bai tanka ba ya yi shu,

’Y/Amshi : Duk ya cika hanya kamar,

: Da tantebur[11] ta yo hawa,

: Da hanzarin noma nis san ka,

: Taho gida rana ta hwaɗi,

: Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

(Amali  Sububu: S/Noman Garin Magaji)

 

Mai sauraren waɗannan ɗiyan waƙar zai ga kamar ga wani rincimemen mutum nan ya kwaso kayayyaki daban-daban ya nufi gona watakila har ba a iya ganin fuskarsa kamar dai yadda mawaƙin ya nuna.

 

A wani wuri kuma

Jagora : Yaro bai san kahon-kaho ba,

: Kuma bai san caɓon-caɓo ba,

: Kuma bai san gumi-gumi ba,   

: A kai jubuha ba ka da hatsi,   

: Ba ka da komi cikin ruhewa,

: Bisa ruwa ƙasa ruwa,

: Sannan ga noma ba ta tashi,

: Sannan ciwon cikin,

: Maza ya ke,

’Y/Amshi : Sai ka ga ƙato,

: Da shi da Maiɗakinai[12] an yi shu.

: Da hanzarin noma nis san ka,

: Taho gida rana ta hwaɗi,

: Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

(Amali  Sububu: S/Noman Garin Magaji)

 

Haka kuma a waɗannan ɗiyan waƙar ana ganin zayyanar wani mutum da matarsa a zaune, ga alama sun sami kansu cikin wani tashin hankali saboda rikirkicewar lamari, har sun kasa yin magana da juna.

 

Akwai irin waɗannan wuraren sosai a ciki waƙoƙin Amali  Sububu, saboda irin ƙwarewarsa da iya sarrafa maganganunsa don mutane su amfana.



[1] Bunguɗu  a cikin kundin bincikensa na digiri na uku a UDU  Sakkwato ne ya kawo.

[2]  Abin bugu, misali wata sanda ko gwami.

[3]  Rugawa da gudu Musamman idan wani yana biye da mutum.

[4]  Bugu da ƙarfi ta hanyar amfani da wani abin bugu kamar sanda ko gora.

[5]  Wannan ma wani nau’in duka ne na rashin tausayi.

[6]  Sayarwa.

[7]  Dafaffen ganye kamar zogale ko tafasa ko rama.

[8]  Dafaffen ganyen dankali.

[9]  Mai sayar da abinci wadda take da yara masu yi mata aikace-aikace.

[10]  Zai tafi/ zai je.

[11]  Babbar motar ɗaukar kaya.

[12]  Matarsa.

Post a Comment

0 Comments