Ticker

6/recent/ticker-posts

Ar Rabbi - Rabbi

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Ar Rabbi - Rabbi

Ar Rabbi – Rabbi,

Ar Rabbi Ta’ala,

Ubangiji tun da nake bara,

Ban taɓa babu ba,

Sai a gidan Munkaila,

Munkaila ya tafi gona,

Na bi shi gonar tashi,

Na mangare shi da ɓota,

Ya faɗi ba daidai ba,

Yana ta amaye-amaye,

Ya yo aman allurai,

Allurai guda nawa?

Allurai guda bakwai,

Na kwashi alluran nan,

Na kai ma sarki duna,

Sarki Duna ya kalli kamata,

Kamata ta hi ta yaro,

Kamata ta hi ta babba,

Ko a hanyar kurmi,

Goro ya hi magarya,

Magarya ta hi dabino.


Post a Comment

0 Comments