Ticker

6/recent/ticker-posts

Idi Hwalalen Karo

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Idi Hwalalen Karo

 

 G/Waƙa: A gaishe ka na Amadu,

: Idi hwalalen[1] karo.

 

 Jagora: Nagode daɗa na gode.

 ‘Y/ Amshi: Barkar ka da rana.

 

 Jagora: Samari ayo anniya.

  ‘Y/Amshi: A zan taushe hakin dawa.

 

 Jagora: ‘Yan samari ayo anniya.

 ‘Y/ Amshi: A zan taushe hakin dawa,

: A gaishe ka na Amadu,

: Idi hwalalen karo.

 

 Jagora: Gaida Idin ɗan Daudu.

 ‘Y/ Amshi: Baya wargi da kashin[2] haki,

: A gaishe ka na Amadu,

: Idi hwalalen karo.

 

 Jagora: Na ga kanyi,

 ‘Y/ Amshi: Mu zauna kiɗi kamar,

: Baya da attaka[3],

: A gaishe ka na Amadu,

: Idi hwalalen karo.

 

 Jagora: Madallah Idi.

 ‘Y/ Amshi: Ya yi taimako,

: Zaman bamu kuɗi yakai.

 

 Jagora: Godiya daɗa kai taimaka.

 ‘Y/ Amshi: Zaman bamu kuɗi yakai.

 

 Jagora: Lawali na gode maka.

 ‘Y/ Amshi: Zaman bamu kuɗi yakai.

 

 Jagora: Kadiri na gode maka.

 ‘Y/ Amshi: Zaman bamu kuɗi yakai.

 

 Jagora: Samari ayo anniya[4].

 ‘Y/ Amshi: A zan taushe hakin dawa.

: A gaishe ka na Amadu.

: Idi hwalalen karo.

 

 Jagora: Wagga gona ta faɗi.

 ‘Y/ Amshi: In akwai wata a gwada mana.

: A gaishe ka na Amadu.

: Idi hwalalen karo.

 

 Jagora: Kyawun noma ya tsarema awo.

 ‘Y/ Amshi: A zan tsarema awon tiya,

: A gaishe ka na Amadu,

: Idi hwalalen karo.

 

Jagora: A gaida Idi,

‘Y/ Amshi: Ɗan Daudu.

: Ba ya wargi da kashin haki.

: A gaishe ka na Amadu,

: Idi hwalalen karo.

 

 Jagora  : ‘Yan samari ayo anniya,

  ‘Y/ Amshi: A zan taushe hakin dawa.

: A gaishe ka na Amadu,

: Idi hwalalen karo.

 

 Jagora: Ga wurin tserewa maza.

 ‘Y/ Amshi: A zan bamu dame-dame[5].

 

 Jagora: Kyawon noma ya tsare awo.

 ‘Y/ Amshi: A zan tsare awon tiya,

: A gaishe ka na Amadu,

: Idi hwalalen karo.



[1]  Dutsi mai faɗi wanda ake amfani das hi wajen shanya ko sussuka.

[2]  Noma yake nufi wato nome hakin da ba a so a gona.

[3]  Moriya.

[4]  Kar a ɓata lokaci.

[5]  Ɗaurin zangarkun gero ko na dawa.

Post a Comment

0 Comments