Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Amadu giwa

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Na Amadu giwa

 

G/Waƙa: Ƙane mutun ko ya ƙi ka,

: Baya ce maka raggo.

 

 Jagora  : Kai mutun ko ya ƙi ka,

: Ba ya ce maka raggo.

  ‘Y/ Amshi  : Tunda har yanzu ba ka tai,

: Biɗar dami ga mutun ba.

: Sannu da sauran haka na Amadu giwa,

: Gogarman Tumba ya gwada masu noma.

 Jagora: Haba maza ku yi noma.

 ‘Y/ Amshi: Ku zan aje mana gero,

: Wanda bai aje gero ba,

: Ban buga masa turu .

: Sannu da saran haki na Amadu giwa,

: Gogarman Tumba ya gwada masu noma.

 

 Jagora : To ashe yaro.

 ‘Y/ Amshi: Baya citta baya mazuru,

: Tunda bai saba kai duhu ba ga noma,

: Sannu da saran haki na Amadu giwa,

: Gogarman Tunba ya gwada masu noma.

 Jagora: To ƙane ya ce ran juma’a,

 ‘Y/ Amshi: Kana ta biɗa ta,

: To Allah ya kai mu juma’ar ga mu gaisai.

 Jagora: Ƙane mutun ko ya ƙi ka.

 ‘Y/ Amshi: Baya ce maka raggo,

: Tunda ba ka zo biɗar dame ga mutun ba.

 

 Jagora: Ƙane mutun ko ya ƙi ka,

 ‘Y/ Amshi: Ba ya ce maka huntu,

: Tunda ba ka je biɗar tuhwa[1] ga mutun ba.

: Sannu da saran haki na Amadu giwa,

: Gogarman Tunba ka gwada masu noma. 

2.5.11  Salau Ɗan Nanaya

  G/Waƙa: Ya yi gargare[2] inda noma,

: Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.

 

 Jagora: Ka biya na mata na Salmo.

 ‘Y/ Amshi: Kar ka fasa noma na Garba.

 

 Jagora: Sai dare na mata na Salmo.

 ‘Y/ Amshi: Kar ka hwasa noma na Garba,

: Ya yi gargare inda noma,

: Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.

 

 Jagora: Ɗan amale ya zan amale,x2

 ‘Y/ Amshi: Shirya Salau ka gado Nanaya,x2

: Ya yi gargare inda noma,

: Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.

 

 Jagora: Ɗan yaƙubu.

 ‘Y/ Amshi: Yana inda noma,

: Bai kula da rana ba daji.

 

 Jagora: Ɗan amadu,

 ‘Y/ Amshi: Yana inda noma,

: Bai kula da rana ba daji.

: Ya yi gargare inda noma,

: Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.

.

Jagora: Tun ba a daɗe ba,

: Ba a jinjima ba,

‘Y/ Amshi: Ba a jinjima[3] ba,

: Zuwa guda Salau ya yi doki.x2

 

 Jagora: Ɗan Nanaya.

 ‘Y/ Amshi: Ya bamu doki,

: Daɗa  a bamu tauna ta dokin.

 

 Jagora: Yaƙubu yana taimaka man.

 ‘Y/ Amshi: Saboda kai Salau ya biyani.

 

 Jagora: Abubakar yana taimaka min.

 ‘Y/ Amshi: Saboda kai salau ya biya ni.

: Ya yi gargare inda noma,

: Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.

 

 Jagora: Ka biya ni mata na Salmo,

 ‘Y/ Amshi: Kar ka hwasa noma na Garba,

: Ya yi gargare inda noma,

 

 Jagora: Sai dare na mata na Salmo,

 ‘Y/ Amshi: Kar ka hwasa noma na Garba,

: Ya yi gargare inda noma,

: Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.

 

 Jagora: Ɗan amale ya zan amale,x2

 ‘Y/ Amshi: Shirya Salau ka gado Nanaya,x2

: Ya yi gargare inda noma,

: Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.

 

 Jagora: Na naya na yaba maid a girma,x2

  ‘Y/ Amshi: Saboda kai salau ya biya ni,x2

: Ya yi gargare inda noma,

: Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.



[1]  Tufafi/Sutura.

[2]  Datsin kuyye da manoma kan datsa domin a rage tsawonsu wajen noma.

[3]  Daɗewa.

Post a Comment

0 Comments