Ticker

6/recent/ticker-posts

Aminaina Ta Samir Aminu Musa

1) Bisimillahi majidi,

    Taimake ni karimi.

2) Nai nufin waƙe a kaina,

      Rayuwata na ga ilmi.

3) Duniya ni ta yi ƙunci,

     Wanda nib ba muƙami.

5) Can cikin zuci da fayi,

     Wai ka ji shi shina balami.

6) Ya Ilahu ka ban habibi

     Wanda zai riƙan da ƙaimi.

7) Mu yi ɗa'a gun ka sarki,

      Tsare mu da bin su mami.

8) Na dubi waɗansu nawa,

      Ƙila sun sam muƙami.

9) Ko ko dai baƙosani ne,

      Aka nuna haɗi da tagumi.

10) Wansu na riƙe fal aboki,

        Aka koma  ko kalami.

11) Ƙila ko don ban da naira,

Dole ko in ƙara ƙaimi-

12) Ga biɗa in kare yawa,

        Kar na zam tamkar ƙazami.

13) Kar ka yo cuta ga kowa,

Nemi son Allah a komi.

14) An yi watsi da old aboki,

        Ba tunawa bubu komi.

15) In Ilahu ya ce ka zamto,

        Babu mai iya ɓata komi.

16) Ya Ilahi ka ba ni baiwa,

        In yabon ɗan nan salimi-

17) Wanda shi ab ba kamarshi,

         Wajen bauta haɗa da komi.

18) Duka mai son ka ka so shi,

        Dubi Jalla ka miƙa komi.

19) Ni Samirun nan faƙirun

       Gun Ilahu da ad da komi-

20) Nai tunani nar rubuta,

Da isar yaddar karimi.

Samir Aminu Musa

Name: Samir Aminu Musa
Email: samiraminumusa95@gmail.com
Phone Number: 08109474995

Post a Comment

0 Comments