Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Muhammadu Hambali Junju

An haife shi a 1936 a Junju da ke ƙasar Nijar. Ya fito daga tsatson zuriyar Shehu Ahmadu Baba, shahararren Waliyyi, ƙasaitaccen masani na Jami'ar Tumbuktu, wanda ya gadi sarauta da malanta. 
Ya fara binciken kalmomin fasaha da kimiyya na Hausa a yayin da ya ke ɗalibta daga 1960 zuwa 1961 a Jami'ar Dakar da ta Alƙahira. 
Ya kammala digirin da na uku a Kasko cikin watan Yuli na 1967 da gagarumin yabo. An wallafa littafinsa na farko a 1968.
Ya yi aiki a Jami'ar Kiki daga 1972 zuwa 1974. A Jami'ar Ahmadu Bello kuwa daga 1974 zuwa 1979 da kuma 1982 zuwa1984. Ya jagoranci Cibiyar Nazarin Hausa da ke Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato a 1984. Ya gabatar da ayyuka masu tushen kansu bila adadin. Ƙwararre ne a fagen mallakar harsuna fiye da ƙima da suka danganci rayayyu da ma waɗanda suka gushe.
Ya jagoranci tarurrukan ƙasashen duniya game da kalmomin kimiyya da ilimin fasaha na Hausa.
Masani ne gaya a fannin ilimin ƙabilu da ilimin ɗan'adam da ilimin halin zaman jama'a da al'adu da magungunan Afirka da nazarin harshen Masar. Kaɗan ke nan daga cikin tarihinsa. Neman ƙarin bayani a tuntuɓi ƙwararru a wannan fage kamar Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau da Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza.
Daga
Dr. Adamu Rabi'u Bakura
Tarihin Muhammadu Hambali Junju:

Post a Comment

0 Comments