Ticker

6/recent/ticker-posts

Almajirin Bara

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Almajirin Bara

 Jagora: Ya ta’ala lillah almajiri bara.

 Amshi: Ya ta’ala lillah almajiri bara.

 Jagora: Wa in bara wa in banbance wa in khairi zalika.

Amshi: Ya ta’ala lillah almajiri bara.

 Jagora: Baƙon da baya sallama mugu ne daga bayan gida yake.

 Amshi: Ya ta’ala lillah almajiri bara.

 Jagora: Yanzu ta kai ga hura.

 Amshi: Ya ta’ala lillah almajiri bara.

 Jagora: Inna koway yi sadaka Allah zai biya masa.

 Amshi: Ya ta’ala lillah almajiri bara.

 Jagora: Inna ina bara kina ƙyale ni ko ɗanɗanki nit taɓa.

 Amshi: Ya ta’ala lillah almajiri bara.


Post a Comment

0 Comments