Ticker

6/recent/ticker-posts

Mata Dangin Fatsima;

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Mata Dangin Fatsima;

 Jagora: Lansika inna lansika,

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Mata dangin Fatsima,

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Ku taru ku bamu na Annabi,

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Kowab bamu na Annabi,

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Allah na gode mashi,

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Annabi na gode mashi,

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Ya shafa mana lafiya,

 Amshi: Kulle.


Post a Comment

0 Comments