Ticker

6/recent/ticker-posts

Ali Na Mani

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ali Na Mani

G/Waƙa: Kar ka raina noma,

: Kullum bari shakkun yi nai,

: Mai wadata noma,

: Zaki na Mani Ali.

 

Jagora: Mai wadata noma,

: Zaki na Mani Ali,

: Kar ka raina noma,

: Kullum bari shakkun yi nai.

  ‘Y/ Amshi: Goje irin halinai ba,

: Ɗai da halin yaro ba,

: Gungurun ƙashin zaki,

: Ya wuce taunar karnai[1].

 

  Kirari: Ma’udu na ɗan yar kunfari Ali na mani,

: Na Abdulmudallib cama,

: Mai ɗaukar mawaƙa,

: Sai kai mai awarwaron tsari,

: Giwa mai hana sauri ,

: Ali na mani Ali,

: Na ɗan hajari ka ki dangin shehu,

: Mai jan giwa zaki mai hana sauri,

: Ɗan malan gaba da baya,

: Sarki Ali ɗan mutan Jibiya,

: Halinka noma Ali na mani.

  ‘Y/Amshi: Goje irin halinai,

: Ba ɗai da halin yaro ba,

: Gungurun ƙashin yaro,

: Ya wuce taunar karnai,

: Kar ka raina noma,

: Kullun  bari shakkun yi nai.

 

  Jagora: Ali ɗan mutan Jibiya halinka noma,

: Nasan ba mai cewa,

: An haihe ka cikin raggaye,

: Kai ko waɗanga masu halbin giwa,

: Na wahalar banza,

: Gata ta yi kwance ga hili,

: Ba ta yin komai giwa,

: Ga ta ta yi kwance ga hili,

: Ba su yin komai,

: Kuma ga ba ka ga hannu,

: Ba su gane wurin halbi ba.

  ‘Y/Amshi: Kar ka raina noma,

: Kullun bari shakkun yi nai.

 Jagora: Wajen maza da mata aiki kag gado,

: Damana da rani bai saba zama ba.

 ‘Y/ Amshi: Arma masu  cewa raggo kai tahi,

: Kai ar tahi an raina ka,

: Mai kantin gona Ali na dolen kande,

: Ba shi jaddawa kande,

: Aron ɗan auta,

: Mai kantin gona,

: Ali na dolen kande,

: Bashi jaddawa kande,

: Aron ɗan auta,

: Kar ka raina noma,

: Kullun bari shakkun yi nai.

 

Jagora: Ali mijin hajiya Kulu,

: Gulbi sha iba,

: Ali mijin hajiya Ige,

: Gulbi sha iba,

: Kwaz zo gareka ya bar cewa,

: A biɗo mai guga,

: Matan gidan na alhaji Musa,

: Igiyar ango,

: Dud duniyar kowa bai fiku ba,

: Mijin kirki ba.

  ‘Y/ Amshi: Kar ka raina noma,

: Kullun bari shakkun yi nai,

: A’a ɗan maza ke kuri,

: Bai kai ga dame tari ba,

: Mai cewa bana bai noma,

: Hatsi sai ka da kyale wawa,

: Wadata ka shirin kaɗi[2] nai,

: Kar ka raina noma,

: Kullun bari shakkun yi nai.

Jagora: A’a ɗan maza ka kuri,

: Bai kai ga dame tari ba,

: Mai cewa bana bai noma,

: Hatsi sai ka da ku kyale wawa,

: Wadataka sherin kaɗi nai,

: Tunda ka yi wawan gandu,

: Biɗi babban walki,

: Biɗi babban walki,

: Kuma biɗi babbar galma,

: Biɗi babbar galma,

: Kuma biɗi babban kwashe,

: Ko da yaushe kaz zo gona,

: Ka yi bakin ranka,

: Ai mahaukaci ɗai ka tara ɗan gayya,

: Nac ce ai mahaukaci ɗai ke tara dawa.

  ‘Y/ Amshi: Kar ka raina noma,

: Kullun bari shakkun yi nai.

 

  Jagora: Yaushe sayen gona,

: Yaushe sayen manda,

: Don bai kula ƙugu[3] nai,

: Ƙugu na yi mai ciwo,

: Zaki ɗan Hussaini,

: Sai dai ya ci tsibin aikinai.

 

 ‘Y/Amshi: Kar ka raina noma,

: Kullun bari shakkun yi nai,

: Mai wadata noma zaki na Mani Ali,

: Ali na mani kotoko,

: Dan galma ga zamani gamji,

: Yau sun  bani sun lalace,

: Giwa ta wuce halbi[4],

: Kai yaro bari wasan banza,

: Giwa  ta wuce halbi,

: Kai yaro bari wasan banza,

: Kar ka je ka jawo,

: Babbar rigima don kanka,

: Babban gida na alhaji Roro,

: Na bakin kwalta,

: Shi ka ba mutun gero,

: Sai ka yi mamakin ka,

: Ba mutun dawa,

: Bari mamakin ka,

: Babban gida na alhaji Roro,

: Na bakin kwalta,

: Shi ka ba mutun gero,

: Ya yi mamakin ka,

: Ba mutun dawa ya yi mamakin ka.

  ‘Y/Amshi  : Kyautar da ak kaɗan,

: Jaki ka zuwa ɗauka,

: Kyautar na Ige,

: Mota ka zuwa ɗaukar ta.

 

 Jagora: Ƙara  ba ni gero,

: In ba ka kiɗina sosai,

: Ali na mani,

: Kayan da jakuna su uku ka ɗauka,

: Babban amale[5] in ya,

: Gawurta yana ɗaukar su.

  ‘Y/Amshi: Kar ka rena noma,

: Kullun bari shakkun yi nai,

: Goje irin halinai,

: Bai ɗai da halin yaro ba,

: Kar ka raina noma,

: Kullun bari shakkun yi nai.

 Jagora: ‘Yan maza ku dai riƙe noma,

: Ka bar zamewa,

: Duk wanda bai noma ,

: Bai ɗebe walakanci ba,

: Kowa ya tsaya kurum,

: Yunwa kale mai hannu,

: Ko aleru ba za a yi mai dori ba.

  ‘Y/Amshi: Kar ka raina noma,

: Kullun bari shakkun yi nai,

: Mai wadata noma,

: Zaki na Mani Ali.



[1]  Karnuka.

[2]  Jifa, a nan yana nufin wadata ce zata jefe shi wato babu shi babu ita.

[3]  Kwankwaso/Kunkuru/Ƙugu.

[4]  Harbi, misali da kibau.

[5]  Raƙumi wanda ya gawurta.

Post a Comment

0 Comments