Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Sarkin Noma Muhammadu

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Waƙar Sarkin Noma Muhammadu

 

G/Waƙa: Koma Gona Muhammadu,

: Ai muhammadu giwata ne.

 

 Jagora : Namijin iya ban rena ma ba,

: Mai maraba da noma ya zaka[1],

: Na mijin iya ban renama ba,

: Mai maraba da noma ya zaka.

 

Jagora : Ko gobe da kai na mijin iya,

: Ko jibi da kai na mijin iya,

: Namijin iya giwata ne,

: Ɗan audu maza na Abubakar.

 

Jagora: Ina Balarabe babana,

: Ai irin gidan abdu Kwamanda,

: Uban kaliya shi yasa ayimade,

: Ya ce in kiɗa maka doki za ni yi,

: Na kiɗa maka ɗan namijin iya,

: Ai Ɗan abdu Kwamanda lahiya,

: Ai ni abdu baba Kwamanda,

: Ai daure ka biya dokin kiɗa,

: Tunda kai niyya ka biya mai,

: Namijin iya  ban rena maka.

 

  Jagora: Ga mai maraba da noma ya zaka,

: Mamman komi gudan mota ɗan maza,

: In ta zaka sai ta tsaya tasha,

: Ai jirgin bisa sha kundum kake,

: Wanda ab bisa ba a yi mai gada,

: Ɗan Rakiya ka ke giwa sha dahi,

: Balan Balarabe ban rena maka,

: Ɗan Ummaru ɗan namijin iya,

: Irin gidan bakin ayi.

 

 Jagora: Ai matar raggo ta sha bone,

: Ta sha bone tasha arkane[2],

: Ta sha bone,

: Ta ga baƙin bone[3],

: In sahiya ta waye,

: In ta ɗau dawa dangane,

: Sai garka garka zaka bi,

: In ta ishe  mata na ɗaka,

: Ta ce masu mun kwana lahiya,

: Ku baku da kingin ga-daka[4],

: Ai ga-daka ko ba ko kwabo,

: Ai su ce mata ba mu da kingin ga-daka,

: Danga doka ai sabko ya kai,

: Koda kiz zaka an kirɓe dawo.

 

 Jagora: Sai ta hito nan gaba zata yi,

: Hat in ta ishe mata na daka,

: Sai ta ce ma su mun yini lafiya,

: Ai sai su ce mata an tai lafiya,

: Ku ba kuda kingin ga-daka?

: Ku ba ta ga dak ko ba ko kobo,

: Ai maccen da gamu isassa mai miji,

: Tana ɗaka sai namijin daka,

: Sai ta ce mata ga hyaɗin[5] dame,

: In ta hyaɗe an ‘yam mata,

: Sai ta yo gaba sai ta guso haka,

: Da ta aya daka sai reda ɗaka,

: Sai tana ta hwaɗin hu’u un, hu’un,

: hu’u un, hu’u un, hu’u un hu’un,

: In ana haka to mi zata yi?

 

  Jagora: Ko gobe da safe zuwa takai,

: In ta rede ta aza bisa,

: Ta ɗau masakin ɗibar miya,

: Mai biɗad dawa ta kaɗin miya,

: Mai ta zo ciki shi na loma,

: In hiɗin faɗin,

: Ga daɗi,

: Ga yawa,

: Mu dai ta zo ciki,

: Mun kwana lafiya.



[1]  Zo/zuwa.

[2]  Wahala mai tsanani wadda kan sa mutum ya fara fita hayyacinsa.

[3]  Shiga cikin lalura/wuya/wahala.

[4]  Yi wa wasu mutane daka don a sallame ka ko da kuɗI ko da abinci.

[5]  Sussuka wadda ake yi da sanduna ba da taɓare ba.

Post a Comment

0 Comments