Ticker

6/recent/ticker-posts

Sa’idu Na Badako

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin NomaSa’idu Na Badako

G/Waƙa: Kana da saurin noma,

: Jan zakin Dodo gwani,

: Sai’du na Badako,

: Wanda noma nay yarda da shi.

Jagora: Kana gama gona goge na Bello

: Jan zakin Dodo gwani.

‘Y/ Amshi: Sa’idu na Badako

: Wanda noma nay yarda da shi.

Jagora: Kana gama gona

‘Y/ Amshi: Goge na Bello dogo

: Mai gwada gona na Bello

: Jan zakin Dodo gwani.

Jagora: Baba na Amadu.x2

‘Y/ Amshi: Mai tattalin jidat[1] taki ba hwasali.x2

Jagora: Yara mu koma,x2

‘Y/ Amshi: Badako inda raggo bai bayyana ba.x2

: Kana da saurin noma

: Jan zakin Dodo gwani.

 

Jagora: Sa’idu na Badako

‘Y/ Amshi: Wanda noma nay yarda da shi.

.

Jagora: Koni maza kui ta noma

‘Y/ Amshi: Mun so ku tara jad dawa ga masara.

 

Jagora: Maza kui ta noma,x2

‘Y/ Amshi: Mun so ku tara jad dawa ga masara

 

Jagora: Su wane ana son gero, x2

‘Y/ Amshi: Jidat taki nay yi wuya.x2

 

Jagora: A gaishe ku

‘Y/ Amshi: Sannu kade

 

Jagora: Ina haure[2]?.

‘Y/ Amshi: Ga shi tsaye,

 

Jagora: Kamam mota,

‘Y/ Amshi: Kamam mota zata Gusau.

: Wurin aikin masu gari

.

Jagora: Yara wuya aikin.

‘Y/ Amshi: Aikin masu gari.

 

Jagora: Ka so tashi.

‘Y/ Amshi: Ba izini,

 

  Jagora: Daduz[3] zaka yi man doki,

: Ka yi man doki danda biya.

‘Y/ Amshi: Ka yi man doki danda biya.

: Ka sawo sirdi ga ragwama.

 

Jagora: Daudu ni kau,x2

‘Y/ Amshi: In ƙumbule[4] kamaj,

: Jikan Alhajiya.x2

 

Jagora: Daduz zaka sayen kalme,

: Ka sawo kalmen Dodo gwani.

‘Y/ Amshi: Mutun ko da aljani garai.

.: Ya baz zakkuwa,

: Ku kai kuyya tare dashi.

 

Jagora: Mutun ko da aljana garai.

‘Y/ Amshi: Ta baz zakkuwa,

: Ku kai kuyya tare da shi.

Jagora: Baba na Amadu

‘Y/ Amshi: Mai tattalin jidat taki,

: Ba hwasali.

Jagora: Giwa ta tashi mai kare na kallo

‘Y/ Amshi: Daudu kare ko da ya gane ta

: Sai dubi baya isa

: Zaman ta rinjayi kare.

: Kana da saurin noma,

: Jan zakin Dodo gwani,

: Sai’du na Badako,

: Wanda noma nay yarda da shi.

Jagora: Ruwan dare gama-gari su wane

: An saba jan makaɗa

: Dadud[5] munka hito kiɗi.

‘Y/ Amshi: Ya zo can mu yi mai waƙa

Jagora: Kana in munka iso gida.

‘Y/ Amshi: In raba kuɗɗin kiɗin,
: Da ‘yan amshin tare da shi. 

Jagora: Wane in kashe kuɗɗin kiɗin.

‘Y/ Amshi: Ga ‘yan nama tare da shi. 

Jagora: Wane buhun lalle,.

‘Y/ Amshi: Nauyin da muka ɗammani[6],

: Bai yi shi ba.

Jagora: Buhun lalle,

‘Y/ Amshi: Nauyin da muka ɗammani,

: Bai yi shi ba.

 

Jagora: Masu noma muka wa kiɗi.x2

‘Y/ Amshi: Zaman[7] sunal lura da mu.x2

 

Jagora: Masu noma ka sayen doki,

: Su tahi su gama mai kaya

‘Y/ Amshi: Su ga yarinya mai kyawo.

: Su anre ta su ɓoye.

: Wurin da rahwahwa[8] bai ga ta ba.

 

Jagora: Can wurin da sakaka[9],

: Bai ga ta ba.

‘Y/ Amshi: Can wurin da Sakaka,

: Bai ga ta ba.

Jagora: Ta ɗora daka ma gero

‘Y/ Amshi: Ta koma,

: Bakin gado tana damu,

: Mai gida yana kwasad dariya,

: Kamar rogon baba Barau.

: Kana da saurin noma,

: Jan zakin Dodo gwani,

: Sai’du na Badako,

: Wanda noma nay yarda da shi.

 

Jagora: Baba na Amadu,x2

‘Y/ Amshi: Mai tattalin jidat taki ba hwasali[10].

 

Jagora: Baba ya tahi birni.

: Ya ishe Sa’idu can zakin Dodo gwani

: Ya bashi turare tare da kwalin mas

‘Y/ Amshi: Mai teburin kirki,

: Bai kama da teburin

: Jikan Ƙandagara.

 

Jagora: Mai teburin kirki

‘Y/ Amshi: Bai kama da teburin

: Jikan Ƙandagara.

 

Jagora: Na yi mahalki Sa’idu,

: Ya sai mota a-kori-kura jikka ashirin

‘Y/ Amshi: Babur ɗin da ag garai.

: Ya ba Baba ya hau.

 

Jagora: Korau na gode

‘Y/ Amshi: Allah ya ƙara girma

: Ya wata’ala ya ƙara girman

: Mai son makaɗa.

: Kana da saurin noma,

: Jan zakin Dodo gwani.

 

Jagora: Baba na Amadu.x2

‘Y/ Amshi: Mai tattalin jidat taki ba hwasali.x2



[1]  Kwasar wani abu, kamar taki da sauran irinsa.

[2]  Haƙori

[3]  Koyaushe.

[4]  Yin kuri, ji-da-kai, girman kai, ɓata rai.

[5]  Koyaushe.

[6]  Zato.

[7]  Saboda.

[8]  Raggo.

[9]  Sauna, marar aikin yi.

[10]  Babu iyakancewa. 

Post a Comment

0 Comments